SAKI UKU A DAREN AMARCI

SAKI UKU A DAREN AMARCI

Wani matashi ne Allah ya azurta shi da ilimi zamani da kuma na addini, ga kuma Allah ya bashi arziki dai-dai misali.

Sai yanke shawarar yin #Aure, kuma Allah ya hada shi da wata baiwar #Allah da ta kwanta masa a zuciyarsa.

Nan take ya mika mata uzurinsa, tayi amanna dashi, kuma ta karbeshi hannu bibiyu.

Ba da dadewa ba, aka sanya musu ranar auren su. Lokaci yayi aka daura musu aure, sai dai ba'anan gizo ke sakar ba.

Bayan ansha biki an watse, sai abokanan ango suka raka shi gidansa, kuma sukayi ban-kwana dashi.

Cikin dare, sai makwabta sukaji #Amarya tana rangada #ihu, tana cewa yanzu saki na kayi? Nan take #Makwabta suka shigo domin kawo dauki bisa abinda #Amaryar take fada.

Shigarsu gidan, sai sukaji #Angon yana cewa "Na sake ki saki uku (3), kuma ba zaki kwana a gidana ba"

Shike nan, wannan makwabtan suka dauke ta suka kaita ta-kwana a wajensu. Da safe sukace da ita ta tafi wajen iyayenta ta fada musu halin da ake ciki.

Bayan tazo gida ta fadawa iyayenta halin da take ciki, sai mamaki ya kamasu. Sai mahaifin #Amarya yasa aka kira ango, suka shiga ganawar sirri.

Bayan ya fito, sai #Mahaifin #amarya yaje shi waje domin yin bincike, dawowarsa ke da wuya sai ya baiwa #Mahaifiyar amaryar takardar saki uku (3).

Labari ya karade gari, kowa mamaki an saki 'ya haka zalika an saki uwa, ba tare da wani dalili ba.

Hakan yasa masu fada aji na anguwar suka kira shi wannan #Mahaifin amaryar, da ya fada musu dalilin sakin. #Mahaifin Amarya ya kada baki yace "A ranar da aka daura auren 'ya ta, #Mahaifiyarta ta dauke ta cikin sirri ta kaita wajen wani malamin tsubbu, wanda shi wannan malamin tsubbun, ya umarci 'ya ta ta kwabe kayanta, ta kwabe, ya saka hannu ya aske mata gaba, kuma yayi mata wasu rubutu a gabanta. Wanda shi angonta da ya kusance ta, sai yaga wannan rubutu na tsubbu da akayi mata, kuma dalilin haka ya sake ta"

Ya cigaba da cewa "Bayan angon ya fada min haka, na fita naje nayi bincike har zuwan wajen wannan malamin tsubbu, sai yace ai ba 'yar bama, har uwar-ma yasha yi mata, domin wai abinda yayi musu, sihiri ne na mallakar miji. Shiyasa da naji haka, nima na saki ta"

Wannan kadan kenan daga cikin halin wasu matan mu na #Arewa.

Ya-Allah ka bamu mata nagari masu son mu dan Allah, ba dan abin hannun mu ba.

Ya-Allah ka bamu mata nagari, ba masu zuwa wajen Malaman tsubbu ko kuma #Bokaye ba. Ameen!

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA