Nima sunana Halima ko A gida

Wani mutum ne yake yi wa matarsa kuri wai shi jarumi ne. Rannan tafiya ta kama su, ya yi shirin yaki. Suna tafiya cikin wani daji sai ga dan fashi. Ya yi masu tsawa, suka tsaya cik. Da ya zo, sai ya tambayi matar sunanta, ta ce, Halima. dan fashin ya ce: “Kin yi sa’a, ban taba Halima, sunan mahaifiyata ne.”

Ya juya wurin mijin, ya ce: “Kai yaya sunanka?” Sai ya ce: “Wallahi, ni ma ko gida Halima ake kira na kuma ka tambayi matata.”

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA