matsala na da mata

Darajarki Da Mutuncinki Yana Hannunki!

Yake 'Yar uwa, ki sani cewa Jan-Aji Kinibibi, ko kuma Takama ba zai taba kawo miki shakuwa azuciyar masoyinki ba.

'Yan mata zaku ga maza nata bibiyarku domin su ga sun aure ku, zasu bi duk wata hanya domin kun zama matansu na Sunnah.

Amma sai kaga ke mace kina juya shi wai domin yazo yace yana Sonki. Jan-aji, Takama, Kinibibi, Ji-da-Kayi. Ki sani cewa duk wannan huduba ce ta Shaidan La'ananne, wanda daga karshe zai kai ne ya baro kawai, daga baya ki fada dana sani wanda keya ce.

Sai kaga mace ta sami me Sonta tsakani da Allah, wanda zai nuna mata tsabtatatciyar Soyayya, ya baki kulawa, yaso yaga ya faranta miki, yayi alfahari dake, amma sai kaga ke mace kina juya shi domin kinsan yana Sonki. Koda ke kina sonshi, amma sai muggan kawaye suna baki gurguwar shawarar da zaki fada ramin da babu damar fitowa, wannan kawaye da kikaga suna baki wannan shawara na ki juya masoyinki yadda kike so, ki tambaye shi kudi ko kuma wani abu da har zai jefa shi cikin damuwar da zaisa har sai yaje yayi aro, domin shi burinsa yaga ya faranta miki. To ki sani cewa wannan kawaye suna tafiya ne da Uban Gidansu Shaidan.

Shawarata anan shine ga ke 'yar uwa me karatu, inaso kiyi la'akari da wadannan kawaye, ki dube su da kyau duba ta ilimi da nutsuwa, ki ga cewa su wadannan kawaye suna da saurayi kamar naki? Idan babu kuma ki dauke su a matsayin wanda basa son cigabanki.

Soyayyar da kika nunawa Saurayinki a waje kafin aure, to ko shakka babu zai nuna miki acikin gida kuma har abada zai cigaba da nuna miki. Domin baki tsawwala masa Soyayyarki ba, amma idan kuma ki tsawwala mishi, to wasu mazan za suyi hakuri su aure ki, amma idan aka samu lokacin kadan da yin aure, sai kiga auren ya fara tangal-tangal wanda karshe rabuwa ce, Allah ya kiyaye. Su kuma wadansu mazan bazama su aure ki ba, wadansu kuma koda suna Sonki zasu hakura da Son, su juya shi zuwa ga lalata. Domin sun gane cewa ke mace ce me aon abin hannun namiji.

Daga karshe ina kira ga ku mata, ku sani cewa wannan dabi'u da na lissafo su a sama, kaiku kawai zasuyi tashar wahala. Dan haka ki riki masoyink tsakani da Allah, ki nuna masa Soyayya idan har kinason shi, idan kuma bakya son shi ki fada masa tun wuri, domin gaskiya daci gareta, amma fadarta sai yafi zuma dadi.

Ya Allah ka shige mana gaba akan duk wani lamarin mu.

Ya Allah ka bamu mata nagari, su kuma mata Allah ka basu maza nagari.

Ya Allah ka wadata tamu da wadatar zuci, ka kuma bamu lafiya da zaman lafiya da kuma abinda lafiyar zata Ci.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA