LABARIN WANI SAURAYI
Wani matashi ne ya tashi da akidar rashin son Aure har sai yayi kudi.
Allah da ikonsa ya baiwa matashin damar yin karatun Boko har ya kai Dakta ba tare da ya yi Aure ba, ya kuma samu aiki, sannan ya fara batun neman Matar da zai Aura.
Ana haka, sai Allah ya hada shi da
wata Kyakkyawar Yarinya mai hankali da fahimta, sai dai ta fi shi ilimin Addinin musulunci, suka yi Aure aka tare, amma shi Ogan baya son ayi saurin haihuwa, matar kuma sai kokarin fahimtar da shi illar yin hakan amma inaa, ya yi nisa baya jin kira.
Mutumin nan ya rinka baiwa Matarsa magungunan hana haihuwa, haka kuma suka kwashe shekaru 5 zuwa 6 ba tare da an samu albarkar Aure ba, Iyayensa da na Matar kuwa sai kokawa suke.
Wata rana da kansa ya cewa matar shi nadai yana sha'awar karamin
Yaro, amma Namiji ba Mace ba.
To lokacin da Allah ya baiwa matar ciki, sai yayi ta jin dadi, amma yana gaya mata fa, ta tabbatar an samu Daa Namiji, a haka dai ta haifi 'ya Mace bisa yadda Allah ya kaddara, ya kuma rinka kyamar Matar tasa saboda ta haifa masa 'ya Mace.
Da Jaririyar nan ta fara girma sai
kyakkyawar surarta ta fara fita, Allah kuma ya jarrabeshi da matukar son Diyar nan tashi, saboda tsananin kyau da Allah ya bata, ba abinda baya iya saya mata, kuma daga wannan yarinyar sai Allah ya dakatar da haihuwarsu.
Yarinya ta shiga Furamare ta kammala, ta je Sakandare ta kammala babu matsala saboda basira da Allah ya huwace mata, ta shiga Jami'a kuma ta kammala, babanta kuwa sai murna 'yarsa ta girma, ga Ilimi ga kyau ga natsuwa, babu wani halin da za'a ce yarinyar na yi maras kyau.
To ku san Allah da hikima ta yiwa
bawansa jarrabawa ta kowane hali,sai yarinyar nan ta je wani gari ziyarar danginsu, amma akan hanyarta ta dawowa gida sai ta yi hatsarin mota ta mutu.
--------------- --------------- ----
Darasin da na koya a wannan labarin shi ne, bai kamata mu rinka gujewa Aure akan talauci ba, domin Allah ne mai Arzuttawa, bai kuma kamata mu rinka yiwa kanmu zabi na jinsin da Allah zai bamu ba Mace ko Namiji, a maimakon haka mu rinka rokon Allah ya bamu zuri'a mai Albarka.
Ya Allah kasa mufi karfi zuciyar mu.

Comments
Post a Comment