KOSAN NAMA DA KWAI

KOSAN NAMA DA KWAI

Kayan hadi:-

•Wake
•Fulawa
•Kwai
•Albasa
•Attarugu
•Maggi Gishiri, thyme, curry
•Man gyada.

Ki wanke waken ki, ki cire dusar a kai a markado miki kamar markaden kosai, amma ki zuba attarugu da albasa a waken kafin ki kai niqan, sannan albasan ce zaki sa dayawa attarugun kuma dan dai-dai, idan wake gwangwani hudu kika sa sai kisa fulawa gwangwani daya, a kan markadadden waken, sannan ki tafasa naman ki ya tafasu sosai, sai ki sa a blender ki niqa ko kisa a turmi mai kyau ki daka.
Sannan ki kada danyen kwai, kamar guda hudu ko uku ki zuba a kai, sannan ki sa Maggi, gishiri, da curry da thyme yadda zai ji, sai ki buga shi sosai, sai ki dora mai dinki a wuta idan yayi zafi sai ki dinga soyawa kamar yadda zaki soya kosai.
Tun kafin ki gama qamshi zaki ji yana tashi, kunnin maigida kuma sai yayi motsi.

Nasan wasu zasu tambaya ko da me za'a ci?
Za a iya ci da Koko, kunun tsamiya, kunun gyada, kunun acca, ko ma asha da shayi, kuma za'a iya cin shi zalla

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA