KASASHEN WAJE: Skype Ya Kirkiro Tsarin Fassara Harsuna
KASASHEN WAJE: Skype Ya Kirkiro Tsarin Fassara Harsuna
Kamfanin Microsoft ya kirkiro tsarin fassara hirar da masu amfani da Skype ke yi a harshen Ingilishi da Spaniyanci.
Wadda hakan zai faru ne yayin hira ko tattaunawa ta bidiyo a Skype, masu magana da wadannan harsuna za su iya fahimtar junansu.
Wannan na nufin an samu ci gaba wajen fassara harsuna a tsarin Skype.
Gurdeep Pall na kamfanin Microsoft ya ce an samu wannan nasara ne sakamakon bincike na sama da shekaru 10.
Comments
Post a Comment