HANYOYI 21 DA ZAKA RAGEWA ANDROID PHONE JAN CAJI DA CIN DATA

HANYOYI 21 DA ZAKA RAGEWA
ANDROID PHONE JAN CAJI DA CIN
DATA

Kamar yadda kuka sani Android
ba kamar sauran wayoyi
bane, domin ita an tsarata da
manyan abubuwa, sannan da
yawan
application wannan tasa masu ita
suke ta kuka da ita wajen jan
chaji da jan data, to ga wasu
hanyoyi da zaka rage mata jan
chaji na batir dinta.

1. Ka bude"Menu"sanna n ka
nufi"Setting"sa ika
latsa"developer 's
options"sannan
ka tafi can kasa, domin duk wani
seti na wayar yana wurin saika
latsa" Background process
limit"zaka ganshi yana"standard
limit"wato bashida adadin yawan
app da wayar zata bude lokaci
daya, to amma saika takaita,
misali
ta rika bude guda biyu, sabanin
da wajen goma suna budewa
suna aiki. Wannan zaisa batir
naka yayi kwari, amma wannan
baduk android keda wannan ba
sai dai version 4.0.
Bayan ka seta wannan kayi
restart
na android naka, domin ta fara
aikinta nan take.

2. Ka rika rufe bluetooth naka,
kuma ya rika zama a hide, duk da
android ta inganta wannan
bangaren ta yadda koda ka bude
second 120 yake ya koma hide da
kansa. Ako wacce waya haka
yake.

3. Ka rika rufe WI-FI naka da
Hosport naka domin barinsu
abude suna jan caji, domin duk
abinda yake search kuma yayi
connect to dayan biyu
* Ko dai yaja caji kadai
* Ko kuma yaja kudi da caji. Ako
wacce waya haka yake, indai
akwaishi.

3. Ka rage hasken screen na
wayarka, domin yinsa da yawa,
yana jan chaji, zaka gane haka,
idan ka duba hasken BB dana LG,
Ita BB zaka ganshi da haske sosai,
kuma fari ko kuma mai Light
haka, LG zaka ga nata da dan
duhu, domin wanda ya saba aiki
da BB idan ya kalli LG zaiga yana-
yana yake kallo wayar ta yi masa
duhu, mai amfani da LG idan ya
kalli tayi masa haske dayawa.
Zaka
iya akowacce waya

4. Ka rage lokacin da haske yake
dauka, domin yana jan caji, misali
daga 15s, zuwa 5s. Wannan yana
aiki aduk sauran wayoyi

5. Karinka rage mata network
yayin da zakayi chat ko binciken
labarai, amma ka bude shi duka
idan kasan zakayi download,
domin canzashi
kaje"Setting "sai"Data&Sync" ka
shiga saika latsa"backgroun d
data"kana danna shi zaice maka
zai rage maka saurin cin data
wato MB da saurin browse, saika
danna"Yes"to cajinka ma ya zai
kara karfi.

6. Ka rika Unsync na sauran
account naka da nasako yake
shigo maka kai tsaye misali
* facebook
* twitter
* Youtube
* email sms
ka bi step na biyar zaka gansu
saika ciresu, sannan ka rage tura
MMS domin shima yana aiki biyu
* yaja kudi da caji
* ko yaja kudi da MB
Duk wanda ya samu.

7. Ka cire"Du battery
saver"domin lissafinsa yana cinye
caji, shima yana connect ne, ka
cire shi.

8. Ka nemi anti-virus mai kyau
wanda zaka rika Optimize na app
naka, ka rika kulle wasu, ta
cikinsa
idan taka ba version 4.0 bace.

9. Ka caja batir na android naka
tun kafin ya dauke, tun yana
saura
20%, saika maida shi caji.

10. Ka caja batir na android naka
awuri mai kyau, karka yi cajin
batir naka arana, kuma yakasance
yanayin wurin mafi yawan zafin
wurin tsakanin 0-45 degree. Idan
yana yin ya wuce haka, to batir
naka zai samu matsala sosai.

11. Sa wayarka awuri mai sanyi
ko wani abu wanda zai rufeta
yayin da take caji, domin jan cajin
da zafi, misali kamar amota yana
kashe batir, saboda waya zafi
takeyi.

12. Ka cire ta daga"Auto
Sync"wato kamar gmail , Google
Contacts, da sauransu, suna jan
caji.

13. Ka cireta daga"Auto Update
Feature"domin yana cin caji.

14. Ka cire Vibration.

15. Kayi amfani da"Power Control
Widget"domin kowacce android
tana da shi, idan kuma baka
bukatarsu saika ciresu.

16. Ka cire duk wani "Homescreen
Widget"matukar baya maka
amfani.

17. Ka yi Disable na"GPS"naka,
domin yana jan caji.

18. Ka rika amfani da "Airplane
Mode" lokacin da zakayi tafiya,
indai kasan babu mai kiranka
wato kayi" Enable na Airplane
Mode"

19. Idan zakayi amfani da"power
saving apps"to kayi amfani
da"Juice defender"anyi shi cikin
saukin jan caji.

20. Ka rika amfani da Apps da
Games na kyauta, domin samun
saukin jan caji.

21. Ka daina sa themes mai motsi,
ko mai duhu akan android naka
domin yana jan caji.
Allah ya bada sa,a

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA