FA'IDA GA MATA MASU SON GASHINSU YAYI KYAU KUMA YAYI TSAWO.
FA'IDA GA MATA MASU SON
GASHINSU YAYI KYAU KUMA
YAYI TSAWO.
Kamar dai Yadda muka
sani kuma kuma kara
tunatarwa cewa karin
Gashi kowanne irine
haramun ne kuma Annabi
(saww) ya tsoratar da mu
game da Karin kowane irin
gashi, sannan kuma ya
tsinewa duk maccen da
take karin gashi da wadda
ke karawa mutane din.
In shaa Allahu ga hanya
wadda zaki samu gashin
kai ba tare da ke shiga
sahun wadanda tsinuwa
zata fadawa ba kuma in
shaa Allahu ko kan ki
kwalkwal yake kika bi
wannan hanya zaki dace
da Iznin Allah.
A nemi garin Hulba kamar
cokali 4 haka a dafa shi a
cikin Ruwa, ya dahu sosai,
sannan a sauke idan ya
huce, sai a shafa wannan
garin da kuma ruwan a kai.
A cakuda shi sosai da gashi,
zuwa kamar Mintuna 15 ko
29 sai a wanke kan da
sabulun Habbatus-sauda,
ko ta Zaitun.
Bayan an yi wannan, sai a
nemo wadannan
mayukkan; Man
Darbegijya, Zaiti-lauz, Man
Zaitun, Man Ridi, Man
Kwakwa, Man Alayyadi,
Man Habbatussauda.
Idan aka same su, sai a
hada su waje daya, a zuba
su a wani waje rika
shafawa Safe da Rana da
Kuma dare In Shaa Allahu a
wata guda zaki ga abin
mamaki.
Note;
Shi Mataki na Farko Ko sau
biyar akayi shi ya wadatar.
Comments
Post a Comment