•Duk abinda kakeyi daure ka karanta wannan darasin rayuwar•

•Duk abinda kakeyi daure ka karanta wannan
darasin rayuwar•

Wata rana wani malami yana so ya karantar da
dalibansa wani darasi, sai ya sami takardar naira
dubu daya (₦1000) sabuwa fil, sai ya shiga
ajinsu, dama daliban yawansu ya kusan kai dari
biyu......
Shigarsa ajin ke da wuya sai ya daga dubu dayan
yace wanene me son wannan? Sai kowa ya daga
hannu, tunda malamin yaga haka sai ya yamutsa
dubu dayan duk ta kudundune. sai ya sake cewa
to waye kuma me so??? Sai kowa dai ya sake daga
hannu.....
Sai malamin ya aje kudin a kasa yasa takalminsa
ya tattake ta duk tayi dumu-dumu da datti, sai ya
dauka ya daga sama yace to yanzu kuma waye
me so??? Ai kafin ma ya rufe baki yaga hannuwa
dai sun cika aji ma'ana kowa yana so kenan.......
Sai malamin yace yauwa to ku dakata dalibai
dama wani darasi nake son ku koya....yanzu ku
duba duk yadda nayiwa kudin nan bai sa sonta
ya fita daga zuciyarku ba, duk wannan
kudundunewar da dattin dake jikin kudin bai rage
darajarsa da komai ba

—• To haka wani lokaci a
rayuwa Allah yake jarabtarmu muke tsintar
kanmu muna fadi-tashi har mukai ga yamutsewa
da kudundunewa sannan mu sami kanmu a wani
yanayi mai kuncin gaske da rashin samin
mafita.....
wanda har mu rika ji a ranmu tamkar bamu da
wata daraja ko kima

—• to ba haka bane ku sani
cewa komai ya faru dakai, komai wuya komai
tsananin dazaka fuskanta a rayuwarka bazaka
taba rasa darajarka da kimarka wadda Allah ya
ginaka akai ba

—• saboda haka kada ka taba
tsanar kanka. Kai dai godewa Allah mahaliccinka
a duk halin daka tsinci kanka, domin kuwa Allah
yana sane da halin da kake, jarabawa ce kadai in
har ka jure sai kaga kaci jarabawar wanda daga
karshe sai kaga ka sami sakamako kyakkyawa....

~•SHIN KA KARU DA WANNAN DARASIN??? To
kaima wanne daraja zaka baiwa wannan
darasin???

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA