Direba da dan sanda

Wani dan sanda ne ya tsare direba, ga yadda tattaunawarsu ta kasance:
dan sanda: “Ina takardun motarka?” Direba: “Ga su nan.” dan sanda: “Ina lasisinka?” Direba: “Ga shi nan.” (Komai aka tambayi direba yana da shi, dan sanda ya  gaza kama shi da laifi). dan sanda: “To wa ya ce ka rika tafiya kai daya a mota, idan wani abu ya same ka wa zai maida ka gida?” Direba: “Manzon Allah (SAW) ya ba mu wata addu’a, a duk lokacin da zan yi tafiya, idan na karanta ta, mala’iku dubu suna tare da ni.” dan sanda: “Mala’iku dubu a karamar mota? To ka yi obalodi, mu tafi ofis, na kama ka!

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA