DARASI! DARASI!! DARASI!!!
DARASI!
Wani attajirin me kudi da ya shagaltu da duniya, domin duk wata bushasha ta duniya dashi ake damawa.
Watarana, sai ya kira me kula da gidan shi wato (Me-Gadi), sai ya bashi wani kullin abu a leda yace dashi "gashi ka ajiye, idan ka hadu da wanda
yafi kowa sakarci (Sakarai) sai ka bashi.
Nan take ya amsa ya kuma adana shi kamar yadda aka bashi umarni, a kwana a tashi, bayan wasu shekaru sai wannan attajirin ya kamu da rashin lafiya, wanda ta kai da kyar ake ganin zai rayu.
Sai wannan bawan Allah me kula da gidan nashi (Me-Gadi) yazo duba shi asibiti, bayan ya gama yi masa jaje, sai wannan me gida nashi (Attajiri) yace dashi "ni ina ganin kwanaki na sunzo karshe, domin wannan jinya tawa bata tashi bace" Me-gadi ya kada baki ya tambaye shi...
*Shin ka tanadarwa kanka babban gida a can kamar yadda ka gina katafaren gida a nan duniya me AC, Lantarki, Pool, Intanet,?
Attajiri yayi shiru.
*Shin ka tanadawa kanka Motocin hawa kamar yadda ka tara su a nan duniya?
Attajiri yayi shiru.
*Shin ka tanadawa kanka 'Yan Mata kamar yadda
ka tara su anan kuna ta bushasha alhalin babu
aure a tsakanin ku?
Attajiri yayi shiru.
*Shin ka tanadawa kanka kayan alatu kamarsu Guava, Ayaba, Lemo, Kankana, Abarba, Gonda, Tufa (Apple) da dai sauransu?
Attajiri yayi shiru.
*Shin ka tanadawa kanka kayan more rayuwa kamarsu TV, Bidiyo, DVD, Audio Arm, kamar yadda kake ta kalle-kallen duniya da jin kide kide?
Attajiri yayi shiru.
*Shin ko ka gina massalatai da rijiyoyi ko dasa bishiyoyi ko tallafawa marayu ko siyawa masallatai dardumai da Qur'anai?
Attajiri yayi shiru.
Sai wannan bawan Allah yaje shi gida ya dauko wancan kulli da wannan attajiri ya taba bashi akan ya baiwa wanda yafi kowa sakarci (sakarai) sai ya bashi.
Kuma yace dashi kai ne BABBAN SAKARAI.
Idan kunne yaji, to jiki ya tsira, kuma gyara kayan ka, ba zai taba zama sauke mu raba ba.

Comments
Post a Comment