Dan Takarar Gwamna Ya Fice Daga Jam’iyyarsa Ana Tsaka Da Zaben Fidda Gwani

Dan Takarar Gwamna Ya Fice Daga Jam’iyyarsa Ana Tsaka Da Zaben Fidda Gwani

Wani dan takarar gwamna a daya daga cikin jam’iyyu masu san tsaida dan takarar gwamna a jihar Kano ya fice daga jam’iyyarsa ana tsaka da zaben fidda da gwani da jam’iyyun kasar nan ke yi a yanzu ciki kuwa har da jam’iyyar APC, PDP, PDM, DPP, LP. da dai sauran jam’iyyu sama (50) wanda hukumar zabe INEC ta yi wa rijista domin fafatawa a zaben gama gari da za a gudanar a 2015.

Jam’iyyar LP da ke da magoya baya a jihar Kano yanzu haka dan takarar Gwamnanta, Barista Tijjani Muhammad Yakasai ya fice daga jam’iyyar inda ya koma jam’iyyar DPP anan take.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA