AN TAMBAYI MALA'IKAN MUTUWA.

AN TAMBAYI MALA'IKAN MUTUWA.

Baka taba yin kuka ba sanda
kake cire ran dan Adam?

- Sai ya amsa, nayi kuka sau daya,
nayi dariya sau daya, kuma naji tsoro
sau daya..

- Ubangiji yace: Menene yabaka
dariya..?
sai yace wani mutum ne naje daukan
ransa, shi kuma yana fadawa mai
dinka masa takalmi... kayishi mai
kyau yanda zanyi shekara ina sawa,
sai na dauki ransa ba tare da yasa
takalmin ba...

-Ubangiji yace:menene yasaka kuka?
yace sanda ka aikeni dauko ran
matarnan a sahara, bayan ta haifi danta
a lokacin sai nayi kuka saboda ihun da
dan yakeyi ba mai taimakonshi...

-Ubangiji yace: Menene yabaka tsoro?
yace sanda ka aikeni in dauko ran wani
malami, duk sanda nakusanci dakinsa
haskene yake dawo dani, hasken ransa
ya tsoratar dani sanda nazo cireshi...

-UBANGIJI YACE MASA KASAN WAYE
WANNAN MALAMIN..
.???YACE A'A....

-Yace wannan yaronne daka dauki ran
mahaifiyarsa a sahara, Ni Na jibinci
lamarinsa ban barshi a hannun kowa
ba....!!!
ALLAHU AKBAR.
.
Dan uwa ko yar uwa mu mika
lamurranmu wurin ubangiji.
Ya zama majibincin lamarinmu, dan
shi zai wadatamu da komi a rayuwa.
ALLAH ya taimake mu AMEEN...

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA