ALAMOMIN DAUKEWAR JININ HAILA

ALAMOMIN DAUKEWAR JININ HAILA


Idan jinin Haila ya dauke akwai alama da shara'a ta sanya domin yazama shine manuniya akan cewar al'adarki ta dauke.

Wadannan alamu sun kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin kantane, sune kamar haka:

1. Bushewar Farji:

Abinda ake nufi anan shine mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin gabanta ta fito da ita busasshiya bawani jini a tare da ita, to da zarar taga haka to ta tabbata al'adarta ta dauke.

2. Farin Kumfa:

wannan wani ruwane fari mai laushi da yake zuwa karshan al'ada, idan mace ta ga irin haka a karshan al'adarta to ta sani ta kammala.

Wadannan alamomi sune suke nuna daukewar al'adar mace, idan mace bata taba ganin al'adaba sai a wannan karon sai tafara ganin bushewar gaba to kai-tsaye ta samu tsarki basai ta jira farar kumfaba.

Amma idan wacce ta saba ganice sai taga bushewar gaba to malamai sukace zata dan saurara kadan domin jiran farin kumfa, amma jinkirin bazai kai ga fitar zababban lokacin sallah ba.

A dunkuledai kowanne daya daga cikin wadannan abubuwa guda biyu yana nuna samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu alokaci gudaba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata sai tayi wankan tsarki domin taci gaba da ibada.

Domin idan batayi wankaba koda jinin ya dauke mijinta bazai sadu da itaba ba kuma zata yi sallaba, da dai sauransu.

Idan mace taga ruwa mai fatsi-fatsi ko diddiga-diddiga bayan daukewar jinin Haila to kada ta damu taci gaba da harkokinta na ibada, dama matsalar idan ta ganshi a farkon jinine, amma idan a karshen jinine to wannan ba komai.

Ummu Atiyyah mai dakin ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) tace:

((Mun kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi-fatsi da diddiga-diddiga bayan tsarki da cewa wani abune)).

Kuduba Abu Daud Hadisi Mai lamba:307.

Ko kuma Nasa'i, Hadisi Mai lamba: 368,

Ko kuma Ibnu Majah Hadisi Mai lamba:647.

Ko kuma Darimi Hadisi Mai lamba:865.

Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar asuba, amma ba'ace tatashi cikin dareba domin ta duba.

Idan mai al'ada ko mai biki (jinin haihuwa) taga tsarki kafin rana tafadi to sallar azahar da la'asar sun hau kanta.

Hakanan kuma idan taga tsarki kafin hudowar alfijir to tabbas zatayi sallar magariba da Isha'i.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA