TARIHIN MAGABATA NA KWARAI

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Salatin Allah da amincinsa su tabbata bisa Shugaban dukkan bayin Allah, wanda Allah ya kebanceshi daga cikin Dukkan Annabawa da Manzanni, kuma ya kebanci al'ummarsa daga cikin al'ummatai, Kuma ya kebanci Sahabbansa da iyalan gidansa da girma da kusanci mafifici.

Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalansa da Sahabbansa.

Yau insha Allahu zamu dora ne daga inda muka tsaya acikin Darasinmu mai suna:

TARIHIN MAGABATA NA KWARAI.

Mun riga munyi tarihin Sayyiduna Abubakar da Sayyiduna Umar (Allah shi Qara musu yarda).

Yanzu kuma insha Allahu zamu shiga cikin tarihin Khalifa na Uku wato Sayyiduna Uthman bn 'Affaan (ra).

Acikin jerin darussan da zasu biyo baya, insha Allahu zamuyi magana akan tarihin nasabarsa, da Martabobinsa, da ayyukansa, da Siffofinsa, da Khasa'isunsa wato abunuwan da ya kebantu dasu.

Ga wasu Daga cikin Martabobinsa agurguje:

1. Shine kadai mutumin da ya taba aurar 'Ya'ya biyu daga cikin 'ya'yan wani Annabi daga cikin Annabawa (alaihimus salam).

In banda shi babu wanda ya samu wannan martabar tun daga farkon duniya har karshenta.

2. Shine wanda yadi kowa gaskiyar kunya. Kamar yadda Manzon Allah (saww) da kansa ya bada shaida.

3. Shine wanda ya tattara Alqur'ani waje guda azamaninsa.

4. Shine mutum na hudu a shiga Musulunci.

5. Shine wanda Allah ya saukar da ayoyi da dama domin bayyana martabobinsa.

6. Shine wanda Allah ya ambaceshi acikin Alkur'ani cewa shi Mai tsaiwar darare ne, yana Sujjadah da Qiyamullayli, yana tsoron lahira, kuma yana Qaunar samun rahamar Ubangijinsa.

7. Shine wanda Allah ya yabeshi da cewa : Yana Umurni da adalci, kuma yana kan tafarki Madaidaici.

8. Shine wanda Allah ya yabeshi da cewa yana ciyar da dukiyarsa afili da kuma aboye, cikin duhun dare, da kuma hasken rana.

9. Shine wanda yake sauke Alqur'ani gaba daya cikin raka'a guda.

10. Shine mutumin farko acikin tarihi wanda yayi hijira tare da iyalansa baki daya, tun bayan Annabi Loot (as).

11. Shine Khalifan da ya fara daura yaki akan bahar maliya.

12. Shine wanda ya tanadar da kusan mafi yawan guzuri da dawakai alokacin yakin Tabouka.

13. Shine wanda ya sayi rijiyar nan mai suna "BI'IRU RUMATA" daga hannun Yahudawa, ya mayar da ita kyauta ga dukkan Musulmai abirnin Madina.

14. Ranar da ya sayi wannan rijiyar, Manzon Allah (saww) ya kwana yana yi masa addu'a.

15. Shine wanda Manzon Allah (saww) yayi masa bushara da samun Aljannah.

Darajojinsa da martabobinsa suna nan da yawa.

Amma insha Allahu acikin karatunmu na gaba zamu ci gaba da kawo wasu daga ciki, tare da kafa hujjah da hadisai ingantattu daga Manzon Allah (saww).

Salatin Allah da amincinsa su tabbata ga Sahibu Liwa'il Hamdi tare da iyalan gidansa da Sahabbansa.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA