NIKAM INA DA YAN MATA DAYAWA AMMA KO WACE NA TASHI RUBUTA MATA TEX TO DA FARKON SUNANTA NAKE GASU KAMAR

Harafin farko na sunanta shine zanyi amfani
dashi wajen furta kalmar soyayya gareta!!!

> HAFSAT: Hawayen sonki na kwarara daga
idanuwana idan har banji sanyayyiyar
muryar
kiba.



> KØÙLTHÖÜM: Kece kika zamo magani ga
duk wasu zaratan zakakan muyagun
cutattuka
da suka addabi Ruhina na tsawon lokuta.



>UMMIZEE ZEE: Uziri baya kasancewa gareni,
Domin hukumar dake aiki karkashin Ruhina
bazata amince da rashin ganin kiba a duk
harbawar Dakika ta Agogo.



> YUSURA: Ya ma'abociyar Hankali da tunani,
ma'abociyar kyawun asali, babu daga wata
fuska danake gani na dauwama cikin farin
ciki face furkarki.



> AISHA: A bangaren Raina shima abin babu
sauki, domin kuwa baya saurarawa wajen
kara zurfafa kaunarki.



> KHADIJAT: Kece sarauniya mai gudanar da
mulki a cikin zuciyata.



> FATIMA: Furran kaunarki yayi yadon flower
a cikin zuciyata.



> HASSANA: Hasken Annurin kaunarki yakan
haskaka dausayin Ruhina, ayayinda duhu
kan
gaggawar fucewa.



> MIMA: Murmushinki yana kawata
Numfashina, haka kuwa Muryarki na Dimauta
tinanina.



> RABI'ATU: Ragamar Mulkin zuciyata mai
dauke da akalar So Da Kaunarki, na mikashi
gareki sahibata.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA