LBRN WATA mata DA mijinta

Wata mata ce tanason ta
gwada mijinta, taga inhar suka
rabu yaya zaiyi?.
Sai tadauki takarda tayi rubutu kaman
haka,
"mijina gaskiya bana sonka yanzu
jinake na tsaneka bana bukatar
kallon fuskanka gara na kalli
fuskan goggon biri da na kalli
fuskan ka, bana burin jin muryanka
gara na saurayi wakar shata da
naji muryanka, dan haka nayi
tafiyata ka auro wata".......
Sai ta ajiye akan kujeran da yake
falon sannan
takoma bayan kujeran ta
buya...
Mijinta yana zuwa yasamu bakowa
a falon yana kokarin zai kirata sai
yaga takarda akan kujera sai
yadauka yakaranta...
Nan take yafashe da dariya sannan
yadauko
wayansa ya sa akunnensa
yafara cewa,''hello masoyiyata
abun da muka dade muna addu'ar
shi yau yazo.
Yanzu
nadawo daga wajen aiki na samu
wannan lalatacciyar matan nawa
tabar gidana kinga sati mai zuwa
kawai sai
adaura mana aure... Sai yafashe
da dariya ya kara da yawe kijirani
yanzu ina zuwa zamu tafi hotel
muci abinci.....''
Bayan yagama maganganunsa sai
yajuya bayan takardar yayi rubutu
sannan ya bude durowa ya canja
riga ya fita yana waka wannan
baitin....
''SOYYAYYA SO MAI SONKA... ZO
MUJE MUJEJEJE MUJE MUJE...."
Haka ya fita yana wakarsa
fuskansa cike da annuri.
Fitarsa keda wuya matar tafito
tana ta kuka tadauki takardan dan
ganin mai yarubuta......
Sai taga yarubuta.......; Kidaina
boye-boye Kifito dan nariga
naganki abayan kujera, kidafamun
ruwan zafi yunwa nakeji naje
insayo biredi.
cikinsu wa akafi razanawa??

Comments

  1. Wallahi matar akafi raxanawa domin shi mijin tunda ya dauki takardan kafin yakaranta ma yaganta.hhh!

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA