Rage Qibarka anan

Nidai Ina Fama da Matsalar kiba, doman ni ban fice shekaru 20/21 ba, amma idan ka ganni za kace wani dan shekara 40 ko 50 ne. Kuma ni Kibar tawa ta gadoce, doman mahaifiyata tana da kiba sosai. Dan Allah malam A taimakeni da magani, ko shawara da kibar nawa zai rage. Nagode. Daga Wani Bawan Allah. AMSA **** Hanyoyin da zaka bi domin rage Qiba suna da yawa. Akwai hanyoyin da zasu iya cutar dakai (kamar Qwayoyin Asibiti wadanda ake sha don rage Qiba). Akwai kuma wadanda zasu Qara maka lafiyar jikinka, kuma zaka samu kuzari da kuma raguwar Qibar jikinka. 1. Ka yawaita motsa jikinka ta hanyar yin tafiya ko guje-guje ko wasu ayyuka kamar Noma, faskare, da sauransu. 2. Ka rage cin abubuwa masu Maiko kamar naman Saniya, Kitse, Kifi, da sauransu. 3. Ka yawaita cin ganye (Vegetables) da 'ya'yan Itace (Fruits). 4. Ka rika amfani da Mayukan Girki wadanda bassu da Cholesterol. Kamar irinsu Man Zaitun, Vegetable Oil, man Talo-talo, da sauransu. (Ka dena amfani da Man-gyada). 5. Ka yawaita Azumin nafila, kuma ka dena cika cikinka TAP da abinci. 6. Ka yawaita karatun Alqurkani, Zikirin Allah, tsaiwar dare, da kuma Tunani acikin lamarin gamuwarka da Ubangijinka. 7. Ka yawaita Shan ruwan SANA-MAKKI zai Qara maka kuzari, kuma zai zabge maka daskararren kitsen da yake jikinka. Sannan ya gyara maka fatar jikinka. 8. Yawancin masu Qiba sukan yi fama da matsalar toshewar Kofofin jijiyoyin Zuciya. Amma idan kana amfani da Zogale akai-akai zai bude maka duk hanyoyin jini da kuma na numfashi. Kuma zai samar ma Jikinka Vitamins kala-kala masu amfani.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA