nemawa kanka sauki anan
IDAN KANA NEMAN ZAMAN LAFIYA, to ka zauna kai kadai. Kar ka shiga cikin Jama'a. * IDAN KANA NEMAN KUBUTA, to ka kiyaye Harshenka. Kar ka sakeshi cikin abinda ba zai amfaneka ba. * IDAN KANA NEMAN MUTUNCIN KANKA, to ka guji zama da Makaryaci ko Munafuki. * IDAN KANA NEMAN KWARJINI, to ka dena zama cikin Mata, ko Jahilai. * IDAN KANA NEMAN DOREWAR LAFIYAR JIKINKA, to ka dena cika cikinka da abinci. * IDAN KANA NEMAN ILIMI DA YARDAR ALLAH, to ka Qaranta barcinka, da cinka, da mu'amalarka da mutane. * IDAN KANA NEMAN SAMUN NASARA AKAN MAQIYANKA, to a rungumi hakuri da kyautatawa garesu. * IDAN KANA NEMAN CIKAR BURINKA AKAN KOMAI, ka rungumi addu'a da neman za'bin Allah kafin ka fara komai.
Comments
Post a Comment