jonathan

Tallar Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan a Arewacin kasar nan, na neman zama kamar wata jangwamgwama, alakakai, ko kuma tallar turmi, wanda duk da nauyin da yake da shi, a haka mai tallar zai cigaba da zagayawa kwararo-kwararo, har Allah ya sa ya yi gamo-da-katarin wanda zai saya. To daga sannan ne dan talla zai yi hutun gaiyar yawon da ya yi dauke da kayan nauyi a kansa. Idan aka yi waiwayen baya, tun farko sai da aka kai ruwa rana a majalisar dattawa a cikin 2010 kafin daga karshe a amince Jonathan ya kasance shugaban kasa na riko a lokacin da Umaru ‘Yar-Adua ke fama da rashin lafiya. Bayan hawansa kuma, bai wata wahala ba ya zama shugaban kasa inda ya karasa wa’adin marigayi Umaru. Jonathan ya sake cin karo da wata sabuwar tirjiya a lokacin da ya nuna maitarsa a fili ta fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2011. Bayan nasarar da ya samu a zaben 2011, ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru ta yadda za a dade ba a manta da zamanin mulkinsa ba. Sai dai kuma a zamanin mulkinsa da ake ciki ne hare-haren Boko Haram suka yi muni sosai, har ta kai ga kusan a ce dokar tabacin da ake kakabawa a wasu jihohin da abin ya fi shafa, ba ta da wani amfani. A gefe daya kuma ana nuna wa juna yatsa tsakanin jam’iyya mai mulki PDP da kuma jam’iyyar adawa, APC dangane da abubuwan da ke da sarkakiya a Boko Haram. Yayin da Arewa ke fama da rikicin da ke kusa da kassara ta, tuni shiri har ya yi nisa a bangaren ‘yan siyasa masu neman mukamai, musamman ma shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan wanda tun ma bai kai ga ayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba, ake ta aiwatar da wasu abubuwa masu tabbatar da cewa tuni ya daura damarar yakin cin zaben 2015. ‘YAN TALLA DA TASHIN HANKALI Tashin farko dai a bangare daya akwai ‘yan ko-Jonathan-ko-jikin-mutum-ya-yi-tsami, wato wasu hatsabiban daidaikun ‘yan kabilar Ijaw da tantiran tsoffin ‘yan ta’addar yankin Neja Delta masu tallar Jonathan da karfin tuwo. Sun dade suna ikirarin cewa tilas sai ya tsaya takara, ko ana so ko ba a so; kai ko ya ki ko ya so sai ya sake fitowa takara; Idan bai ci zabe ba za a yi yaki; Idan Jonathan bai zarce ba za su balle daga Nijeriya; Idan ya ji tsoro ya ki sake tsayawa takara, to ka da ma ya sake ya koma yankin Neja Delta ya ce zai zauna. Da yake babu wata hukuma mai karfin kashewa ko dakushe kaifin hakoran masu irin wannan kasassabar Magana, ta kai ta kawo har akwai masu furucin cewa, idan aka yi zaben 2015, idan Jonathan bai ci ba, to za su fito domin su yi fito na fito da Arewa. A wannnan bangare ba a tsaya a sahunn tsoffin ‘yan ta’addar Neja Delta ba, abin ya hada har da tsoffin ‘yan alewa irin su Cif Edwin Clark masu cewa, tilas sai Jonathan dan yankinsu ya sake yin shekara hudu, domin su ma su tatsi kindirmon babbar saniyar da ake tatsa sannan su saki su bai wa wani yanki na kasar nan shi ma ya dana. KUNGIYOYI NA SARARI DA NA BOYE Akwai kuma kungiyoyi na sarari da kuma na boye, wasu an sha jin su tun a zaben 2011, wasu ba su dade da fitowa ko kafawa ba, wasu kuma suna ne kawai a takarda da jaridu. Bayan wadanda kuma ake gani da karantawa rututu a shafukan facebook, dukkansu da ke nuna Jonathan ne kadai alheri ga kasar nan. A kullum a jaridu da mujallu da gidajen talabijin sai ka ga ko ka ji wata ko wasu kungiyoyi na tallar Jonathan. A sahun gaba dai ‘yan bangar zamani masu yakar ‘yan adawa da tsinin biro, da kuma kafafen yada labarai, wato Transformation Ambassadors of Nigeria, TAN, wadanda a kullum ke ta kulle-kullen Jonathan ya sake dare kujerarsa a 2015. Su ne ke shan alwashin iya tara sojojin hayar magoya bayan Jonathan bila’adadin. Akwai kuma wata wadda ta yi kaurin suna mai suna Nieghbour 2 Nieghbour, sai G2G, ga kuma irin su Goodluck Support Group. A kwanan baya ne ofishin mai ba shugaban kasa shawara a bangaren al’amurran da suka shafi siyasa ya bayyana cewa zai tantance yawan kungiyoyin da ke ikikarin magoya bayan Jonathan wadanda aka kiyasta sun kusa dubu hudu. Har ma kungiyoyin mata zalla akwai, irin su mata masu hange ko hango wa shugaba nesan da bai hango wa kansa ba; wato, Women of Bision. A shafukan facebook, akwai ambaliyar shafuka da dama na masu goyon bayan Jonathan wadanda suka gwanance sosai wajen yawan rubuta kakkausar suka ga APC da duk wani dan Arewa. Wadannan marubuta, maimakon su kara masa farin jinni, sai ma farin jinin da yake da shi ya ragu ainun a idon ‘yan Arewa. ‘YAN SIYASA NA SARARI Ganin yadda aka shirya tarukan amincewa Jonathan ya fito takarar shugaban kasa a yankin Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Kudu, sai mataimakin shugaban kasa, Alhaji Namadi Sambo ya hakikice sai an kira taron masu ruwa da tsaki da sauran dan dago-dagon furar PDP a makon da ya wuce a Kaduna, domin a goya bayan Jonathan ya sake tsayawa takara a 2015. Wannan taro dai ya ci karo da tangarda domin wasu gwamnoni sun nuna karara ba su goyi bayan Jonathan ba. Taron da aka shirya domin yankin Arewa maso Yamma, wasu gwamnoni dai ba su halarta ba, wasu kuma sun ki amincewa da yi musu karfa-karfar bayyana Jonathan da Ambassada Aminu Wali ya yi inda ya nuna cewa, gaba daya PDP din yankin sun yi na’am da tsayawar takarar Jonathan a matsayin zakaran damben da suka ce zai iya bige APC a 2015. Babbar matsalar da suke fuskanta dai ita ce kasa shawo kan hare-haren kashe-kashe da ke addabar Arewa da Jonathan ya kasa yi, duk kuwa da dimbin kudin da ake ikirarin an kashe ko ake kashewa a fannin tsaro domin dakile Boko Haram. RASHIN DAN TAKARAR PDP DAGA AREWA Wannan kuma wata babbar matsala ce da ake ganin Arewa ke fuskanta a karkashin jam’iyya mai mulki; wato PDP. Rashin dan takara daga Arewa na kara wa Jonathan kwarin guiwar ganin cewa zai iya cin zabe, sai dai kuma hakan ta sa da dama sun mai da hankalinsu ga APC, wacce ake da yakinin cewa dan Arewa ne za ta tsaida. Akwai masu has ashen cewa nan ba da dadewa ba, matukar kashe-kashen da ake yi a Arewacin kasar nan ya ci gaba da munana, to da dama za a gudu daga inuwar Jonathan a fake a inuwar APC. Sai dai kuma da yawan ‘yan Arewa masu goyon bayan Jonathan na masu kafa hujja da cewa matsalar Arewa ba Jonathan ne ya haifar da ita ba, gadonta ya yi, tamkar yadda uba ke mutuwa ya bar wa dansa gado.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA