girkinki sirrinki
Wainar Garin Kwaki Assalamu alayikum makaranta wannan shafi, da fatan kuna jin dadin girke-girken da muke kawo muku a nan. A wannan satin dai zamu kawo muku yadda ake yin wainar garin kwaki. Na san uwargida za ta ce garin kwaki kuma? E garin kwaki, da fatan kin ji da kyau. Na san mutane da yawa sun san wainar rogo, to idan kika sami kan ki a in da babu rogon kuma ko kuma kina neman sauyi to sai ki yi amfani da garin kwaki. Mutane da dama har ma da masu sayar da wainar rogo yanzu da garin kwaki suke yi , saboda tafi saukin yi kuma tafi dadi. Wainar garin kwaki waina ce mai saukin yi, zaki iya yi cikin dan kankanin lokaci. Wannan waina ba ta tsaya ga Uwargida ba har ‘yan makarantar kwana ma za su iya yi domin bata da daukan lokaci kuma kayan hadin na ta ba wani wuyar samu ne da su ba, kuma ba tsada gare su ba. KAYAN DA ZA KI TANADA 1. Jan garin kwaki 2. Attaruhu 3. Albasa 4. Mai 5. Dunkulen knorr 6. Gishiri 7. Man gyada ko man zaitun YADDA ZA KI HADA Ki sami garin kwakinki ja, iya yadda ki ke so yawan wainar ya kasance. Ki dafa ruwan zafi, idan ya dahu sai ki juye a kwano, sai ki kawo wannan jan garin kwakin ki ringa barbadawa a cikin ruwan har sai kin zuba iya yadda kike so. Sai ki rufe kwanon da murfe ki tsiyaye ruwan. Ko kuma a takaice kawai nace ki yi teba. A gefe daya kuma kin jajjaga attaruhunki da albasa, sai ki zuba akan wannan garin, ki kawo gishiri da dunkulen knorr ki zuba akai. Sai ki kawo muciya ko cokali mai karfi ki juya sosai yadda kayan hadin zai juyu sosai, komai ya shiga cikin garin kwakin. Idan kina so ma kina iya juyesu gabadaya a cikin turmi ki daka don ya hadu sosai. Idan kin tabbatar komai ya ji sosai sai ki ringa gutsira kadan-kadan ki saka a tafin hannunki ya yi falai-falai, amma ba falai-falai sosai ba, ki bar shi da dan kauri domin ki sami totuwa idan kin soya, idan ba haka ba kuwa idan ya soyu zaki ga ya yi kayau-kayau, ko kuma kina iya yin duk fasalin da kike so. Sai ki ringa saka wanda ki ka yi akan babban tire, kada ki bari su hadu da junansu,domin idan ki ka hadesu zasu manne ne su damule miki. Idan kin gama sai ki bar shi ya dan sha iska kamar minti goma. Ki dora man ki a kan wuta ki yanka albasa a cikin man, idan albasar ta yi ja sai ki kwashe albasar daga cikin man, alamar man yayi zafi kenan sai suya. Sai ki kawo wannan fale-falen da kika yi na garin kwaki ki ringa sakawa dai-dai da dai-dai a cikin man. Idan ya yi ja sai ki juya daya gefen ma ya soyu. Idan kin gama ki kwashe ki saka wainar a cikin matsami domin man ya tsane gabakidaya. Idan ke mai son yaji ce sai ki ci da yaji idan kuma ba kya son yaji wannan attaruhun da kika saka ya isar miki shi kenan. Ga wadanda ba su san wainar rogo ba ita ma ba wuya ne da ita ba, ita ma dai kamar wainar garin kwaki haka zaki yi ta, sai dai kawai a zamanin nan kowa yana son hutu, Uwargida ba a gaban murhu zata kare ba, amma ga masu son su san yadda ake wainar rogo to bismillah! duk kayan da kike bukata don yin wainar garin kwaki, shi zaki tanada domin yin wainar rogo. YADDA ZA KI HADA WAINAR ROGO Ki samu rogonki ki raba shi gida biyu, rabi da dan kadan ki goga shi, sauran kwatar kuma sai ki dafa shi. Idan ya dahu sai ki kwashe ki zuba a cikin turmi da wanda kika goga din ki hada ki kirba, ki zuba albasa da attaruhu da dunkulen knorr da gishiri ki juya ki cigaba da kirbawa, idan kin tabbata ya yi, hadin komai ya shiga cikin rogon sai ki kwashe a roba ko kwano ki lailayi shi ko ki fakada shi yadda kike so. Idan kin gama ki bari ya sha iska na minti biyar zuwa goma sai ki soya a cikin mai mai zafi . To uwargida zabi ya rage naki duk wanda kike so sai ki yi, ki zaba ki darje, idan baki da kwuiyar daka sai ki yi amfani da rogo, idan kuma ke ‘yar zamani ce sai ki yi amfani da jan garin kwakinki. Amma duk da haka idan kina son ki yi ta rogon amma kina kwuiyar daka kina iya amfani da (food processor) ta kirba miki rogonki, a zamanance kenan.
mungode
ReplyDeletePEN
ReplyDeleteAllah yasaka
ReplyDelete@Teeemah,
ReplyDeleteAmeeeen