mal. lado
Lado ne yaje Abuja wajen kawunshi yaje tun karfe takwas 08:00am sai akace mishi bayanan sai karfe biyu zai dawo, don saiya jirashi, yana zaune har karfe daya tayi, yunwa ta fara damunshi kuma gashi dari biyune kacal a aljihunshi, kuma wajen babu abincin haka saidai hotel. Can sai ya yanke shawara ya tashi ya kakkabe jikinshi ya dawo fes ya dauki jakarsa ya sagala kawai gogan naku cikin kwarin gwiwa ya nufi wani hotel, yana shiga reception room sai receptionist din ta tarbeshi tace wani yake nema ko lodgin yakeso? yace mata lodging yakeso, tace masa to daki daya naira dubu arba'in N40,000, yace bakomai zai biya, aiyaga wajen yanada kyau kamar wanda ya baro ne yanzu a Dubai hanyarsa ta dawowa daga U.S. Saiya tambayeta cewa kudinnashi dollersne baida canji ko zasu iya amsa, tace eh ranka ya dade, ta fara bashi girma, daganan ya tambayeta inda restaurant nasu yake yaci abinci saboda yunwa yakeji, nan da nan ta kaishi tace musu sabon customer ne yanzu ya dawo daga U.S saboda haka su kula dashi, yace akawo mishi abinci 2 bowls na pepper soup, sai kuma catfish, spanish wine dadai sauran abinci haka dai ya zauna ya cinyesu tas. Can sai aka kawo masa bill ya duba yaga kudi naira dubu talatin da biya N35,000, gogan nakufa sai ya fara zufa yacewa mai amsan kudin yaje ya dawo yana hutawa ne, har sau uku yana zuwa yana korarsa, canfa sai ma'aikatan wajen suka fara zarginshi kan cewa baida gaskiya, don haka suka kira mai security sukazo suka zagayeshi, daya daga kai ya kallesu daya bayan daya, kawai saiya matsa wayar aljihunshi ya kira numbar dayan, tana fara ringi ya ciro yace, HELLO, EHH BOMB DIN YANA TARE DANI YANZU HAKA BAN RIGA NA TADA SHI BA..... OK CIKIN MINTI BIYU KO.... TO BA DAMUWA YANZU HAKA MA A INDA NAKE AKWAI MUTANE DA YAWA DON HAKA GA DUKKAN ALAMU ZAMU SAMU NASARA DOMIN ZAI KASHE MUTANE SOSAI......AINI INA ALFAHARI DA HAKAN......TOH SHIKENAN AN GAMA... Haba ai tun kafin ya sauken wayar ma kowa ya watse kamar anyi ruwa an dauke. Dayaga kowa ya watse shima ya fito yayi tafiyarsa. Kalma daya akan Lado. Lolx. Kunga Laifinsa
Comments
Post a Comment