gaskiya. tafi kwabo

ACIKIN WADANNAN MUTANEN WA YAFI GASKIYA Wani Bakano ne yayi aiki ya sami kudinsa har dubu bakwai cif-cif, sai ya rasa inda zai boye kudin sai wata dabara ta fado mishi sai ya tafi ya haka rami ya binne. Bayan ya gama binnewa tafiyarsa keda wuya sai ga wani bazazzage shima yazo da kudinsa zai rufe, cikin ikon Allah sai ya nufi inda bakano. ya rufe nasa sai yakama haka rami ya danyi nisa da haka sai yaga kudi cus, kawai sai shima ya zuba nashi kudin ya hada ya rufe wato dana bakano, bazazzage yayi tafiyarsa. Can anjima sai bakano ya dawo daukar kudinsa bayan ya ture kasa sai yaga kudinsa da wasu kudin kuma, sai bakano yasa hannu ya kirga iyakar nashi ya rufe sauran a inda suke yayi tafiyarsa abinsa. SHIN WAI TSAKANIN BAKANON NAN DA BAZAZZAGEN NAN WA YAFI GASKIYA NE??? IDAN AKACE KA ZABI SARKIN GASKIYA WA. ZAKA ZABA ACIKINSU??

Comments

  1. mustapha isah liman16 April 2015 at 12:53

    gaskiya ko wanne yana da gaskiya

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA