Gaskiya tafi kwabo 2
To ina mai yimaka horo da cewa duk inda xaka ka riki GASKIYA.kada kayarda kayi karya.kada kamanta cewa mai gaskiya yana tare da allah.''sani yay alkawarin cewa xai riki GASKIYA a duk halin da ya xinci kansa. Sani ya nufi birnin kano kwanci tashi har ya nufo wani daji waishi daji falgore.kasan ada babu motoci don haka a kafa yake tafiya cikin kungurmin dajin falgore,bai ankare ba sai yaga karti 5 a gabansa.can sai babansu ya daka masa tsawa yace.''kai ina xaka? sai sani yace ''xani birni cirani'' sai yasake tambayara yace mene ke cikin kunshin daka dauko?? Sai sani yace ''yar curin fura ce kwaya 1 da quli da kuma kudin guxiri masu dan dama'' dajin wnn jawabi sai baban yace kai ku kyale wnn sakaran ya wuce daji tabbabe ne .inba tabbabe ba waxai gayawa barayi ya dauko kudi masu dama cikin kunshi tsumma?sai sani yace maigida ni ba tabbabbe bane da hankalina.in baka yarda ba bari in nuna maka sai ya sauke kaya ya kwance saiga curin fura da quli dakuma kudi masu yawa.sai mamaki
Comments
Post a Comment