ya jibgi mahaifiyar sa
YA DUKI MAHAIFIYARSA Bisa tsare tsarensa na kowace rana sai ya duki matarsa tare da hujjah koh babu. Lamarin dake 6ata ran mahaifiyarsa matuka. Kasancewarsa daa ga limamin garin, hakan yasa iyayen matarsa ke matukar jin nauyin gidansu. A duk lokacin da ta kawo korafi gida, cikin rarrashi ake lalla6arta ta koma tare da nuna mata cewa xa'a samu sauyi nan bada jimawa ba. #Lado mashayi ne, kuma bai juma ba da Mahaifinsa ya rasu a sakamakon matsananciyar ciwon xuciya wanda ya gamu da ita a dalilin dansa Lado. Rannan cikin dare, bayan Lado ya dawo daga yawace yawacensa kamar yadda ya saba har kullum. Ya tarar da mahaifiyarsa tare da matarsa cikin daki guda suna phira har suna shewa. Ran Lado yayi matukar 6aci da abinda ya tarar, a cewarsa, Uwarsa ce take bawa matarsa muggan shawarwari. Don haka nan take ya hau mahaifiyar tasa da duka, ihu matar ta ringa yi amma babu wanda ya kawo musu dauki. Da kyar uwar ta samu ta rarrafa ta bar gidan sannan ta sha. Irin wadannan 'ya'ya Allah kada ka bamu su, Ameen!
Comments
Post a Comment