wata rana

Wata rana akayi musu tsakanin dan sarkin baccin kano da dan sarkin baccin Adamawa. Dan sarkin baccin kano ya kwanta bakin wata fadama bacci ya daukeshi har ruwan damuna yazo ya gangara dashi cikin rafin nan kifi ya hadiyeshi shikuma kifin kada ta hadiyeshi ita kuma kadar dorinar ruwa ta hadiyeshi sai watarana mafarauta suka kama dorinar suka yanka suka fede suka dauko kada acikin cikinta suka fede kadan sai sukaga kifi acikin cikinta suka fede kifin saiga mutum a ciki duk wannan abun da akeyi bai farka ba saida aka tashe shi sannan ya farka yana farkawa sai ya hau fada yana cewa daga fara baccina sai atasheni? Sai shikuma dan sarkin baccin Adamawa. Shikuwa dan sarkin baccin Adamawa ya kwantane a gindin wata bishiya sai ruwan damina yazo ya gangara dashi cikin kogi sai wata rana gabar kogin ta zabtaro ta fada masa a kai daganan sai wata bishiyar kuka ta tsiro akansa kuka ta girma harta tsufa sai wata rana iska mai karfi tazo ta kada bishiyar, mutane suka taru suna kallon kukar sai suka hangi mutum kwance karkashinta aka duba sai aka ga yana numfashi aka sassare sauyoyin kukar aka fito da shi dayaji hayaniyar mutane sai ya farka yana cewa wai mutum daga fara bacci sai a tashe shi? WAYAFI NAUYIN BARCI?

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA