waseeqar soyayya 1

Waseeqar Soyayya 01 NEMAN AMINCEWAR SOYAYYAR KA ! Assalamu Alaikum Warahmatullah" bayan shinfidaddiyar sallama wacce addini na ya tanadar, ya harkokin yau da kullum ? Ya lafiyar ka ? Bayan haka, kada kayi mamakin ganin wannan waseeqa tawa ko kuma shedan ya yaudare ka cewa kada ka amince dani domin nayi tallar kaina a gare ka" sam kada ka yarda da hakan, yazo a hadisan manzon Allah (s.a.w) cewa a zamanin sa mataye suna zuwa ga maxaje suna neman amincewar su domin suyi Aure. Don haka neman SOYAYYAR namiji a wajen mace ba rashin aji bane ko zubar da qima, wannan shine cikakken aji da kyautatawa domin munyi koyi da bayin Allah na kwarai. Suna na xxx, wata kila ka sanni,wata kila kuma baka sanni ba. A wata rana ina tafiya na hadu da kai a hanya. Cikin ikon Allah sai naji na kamu da soyayyar ka sakamakon ganin kamalar ka,ilimi,hankali,iya ado,dss. Zuciya ta ta aminta da kai ta fara azabtar da gangan jiki na! Lallai ina bukatar agaji daga gare ka don haka zan so ka ziyarce ni ta hanyar adireshi na kamar haka ** ** xxx kano state Wata kila idan ka ganni ka aminta dani" idan ma baka aminta dani ba ka amince yin tarayya dani nasan a hankali wani yanayin nawa zai iya fizgar zuciyar ka izuwa ga sona kamar yadda halayen ka suka fizgi tawa izuwa ga son ka. INA NAN INA JIRAN KA A KOWANE LOKACI !!

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA