wasanni

WASANNI:Nijeriya Na Tsaka Mai Wuya Saboda Hukumar NFF Nijeriya na cikin hadarin kasa cika wa'adin da Fifa ta gindaya na ranar Talata domin maido da jami'an hukumar kwallon kasar - NFF wandanda ta cire. Gwamnatin Nijeriya na cikin rashin tabbas ne saboda yajin aikin da ma'aikatan shari'a ke yi. Maudu'o'i masu alaka da wasannin. A makon daya gabata ne Fifa ta dakatar da Nijeriya daga shiga harkokin kwallon kafa saboda zargin gwamnati na katsa landan a harkar kwallon kasar. Sai dai gwamnatin ta ce ta cire jami'an NFF ne bisa umurnin wata babbar kotu a jihar Filato. Idan har Nijeriya ba ta maidoda shugabannin NFF, a karkashin jagorancin Aminu Maigari ba, to kasar ba za ta halarcin gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20 da ake soma wa a watan Agusta a Canada.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA