wakan janaba
YADDA A KE WANKAN JANABA ************************ da farko zaka fara kar kato botikin da yake gabanka bayan ka shiga da ruwa matsaftaci, Sai ka wanke hannunka sau uku, Sai ka wanke duk kan inda najasar ta shafa, San nan sai kayi tsarki, alokacin da zaka yi tsarki a lokacin zaka ɗaura niya a zuciyarka/ki. San nan sai ka ɗaura alwala kamar yadda kake yi a kowace sallah, ƙafa ce kawai baza ka wanke ba. San nan sai ka tsoma hannunka cikin ruwan sai ka murza a kanka ka tabbata ko ina ya samu har sau uku,(saboda a lokacin da janaba ta sameka kofofin gashin jikinka budewa sukeyi idan ka kwara ruwa akanka zai iya yi maka illa shiyasa akafiso ka tsoma hannunka ka murza a kanka dan kafofin gashin su rufe). San nan sai ka ɗebo ruwa ka dinga kwarawa ɓarin gefen jikinka na dama kana cuɗawa ko ina ya samu, sannan ka wanke gefen jikinka na hagu shima ka cuɗa ko ina ya samu. Idan kagama wanke jikinka duka da ruwa san nan sai ka wanke ƙafarka cikon wannan alwala da ka fara. Shi ke nan ka ko kin kammala wakan Janaba. Namiji haka zaiyi! Mace haka zatayi! Wankan Biki haka zakiyi Wankan Haila haka zakiyi Wankan Jumu'a hakane Wankan Idi shima hakane Ban bancinsu kawai niya. ALLAH YASA MU DACE AMEEN.
Comments
Post a Comment