tsuntsu da annabi musa
Wata rana Annabi Musa yana zaune sai yaga wani tsuntsu mai kyawun gaske ya shiga cikin tabo sai jikinsa ya baci ya koma yayi muni, sai tsuntsun ya shiga cikin ruwa ya wanke jikinsa sai kyawunsa ya dawo. yayi tayin haka har sau biyar, sai mamaki ya kama Annabi Musa, yace Allah kasa sanar dani fassarar abinda wannan tsuntsu ya aikata, sai Allah ya sanar dashi cewa kamar haka al'ummar Annabi muhammadu zasu dinga aikata zunubi amma da zarar sunyi sallah ta farilla to wannan zunubi ya goge kamar yadda wannan tsuntsu yake wanke jikinsa. Allah yasa mu dace....
Comments
Post a Comment