s. a. w
Wata rana Annabi ya wuce ta wani waje sai yaga ana ganawa Bilal azaba, ran Annabi bai yi dadi ba. Ya samu Sayyadina Abubakar yace masa, Ya Abubakar lallai ana azabtar da Bilal saboda Allah. Sakamakon kaifin hankali irin na Abubakar sai ya fahimci abin da Annabi yake nufi, kai tsaye ya je gida ya kwashi kudi makudai ya tafi wajen Umayyata bin Khalaf yace masa, shin zaka sayar min da Bilal? Yace kwarai kuwa mai zanyi da wannan wulakantaccen bawan. Ya tsugawa Abubakar kudi, amma Abubakar ko ragi bai nema ba ya zaro kudi ya bashi, la’asar na yi Abubakar ya je wajen Ka’aba ya bada sanarwar cewa ya sayi Bilal kuma ya ‘yantashi saboda Allah. Shi yasa duk lokacin da aka ce Abubakar shugabanmu, to sai Umar ya kara da cewa “KUMA WANDA YA ‘YANTA SHUGABANMU BILAL”… Allahu Akbar, Allah ya kara yarda da kai Ameen.
Comments
Post a Comment