naija
Boko Haram Sun Kashe Mutane 45 A Jihar Borno Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne a jiya Litinin sun kai hari wani kauye da ake kira Dille da ke jihar Borno, inda suka kashe mutane sama da 45 tare da kona gidaje, wuraren ibadu da shaguna, wanda hakan ya sa jama'ar garin kauracewa gidajensu suka shiga daji domin tsirar da rayuwarsu. Bincike ya nuna cewa 'yan bindigan sun shigo kauyen ne da jerin gwanon motoci sama da ashirin yayin da wasu kuma ke kan babura. Kamar yadda wani mazaunin garin mai suna Njimtiku Papka, wanda ya bayyanawa manema labarai a Meduguri ta waya cewa 'yan bindiga sun yi ta harba bindiga ne kan mai uwa jawabi a yayin da duka shigo kauyen.
Comments
Post a Comment