mutum
MUTUM NA IYA SAMUN RABONSA TA HANYAR HARAMUN....... Watarana Sayyadina Aliyu Ibn AbiDalib yaje wani gari sai ya tsaya kofar wani masallaci domin yin sallar walaha dan haka sai ya kira wani yaro ya bashi rikon dabbarsa rakumi ko doki ya shiga yana shiga sai yaronnan yaga cewa lalle wannan igayar da aka daure dabbar idan an kaita kasuwa za'a samu kudi mai dan kauri dan haka sai kawai ya kwance igiyar ya gudu kasuwa da ita koda Sayyadina Aliyu ya fito yaga haka sai samu wani bawan Allah kuma yace masa akwai yaro mai kama kaza kaza ka bishi ka sayomin igiyar dabbar dake hannunsa ka dawo ni kuma na baka riba mutumin yabi yaro ya kuma same shi ya taya igiya darhami daya shi kuma ya sallama masa ba wata gardama yana zuwa yayima sayyadina Aliyu bayanin yadda sukayi sai kawai Sayyadina Aliyu yace Allahu Akbar kaga ya ci rabonsa ta hanyar haramun domin kuwa dama nayi niyyar da ace ya tsaya na gama na fito to zan bashi kyautar dirhami guda to amma gashi yanzu ya samu dirhamin amma kuma ta hanyar haramun kuma Irin wannan ka iya sawa mutum ya fada cikin WUTAR JAHANNAMA. ALLAH KASA MUFI KARFIN ZUCIYOYINMU KA KUMA BAMU IKON CIN RABONMU TA HANYAR HALAL.
Comments
Post a Comment