muna rokon allah baya amsawa
MU NA ROKON ALLAH BA YA AMSAWA?. Wata rana Ibrahim bin adham ya gifta ta cikin kasuwar basara, sai mutane suka ce masa "ya aba ishaq, muna roqon Allah baya amsawa, sai yace" qila zukatanku sun qeqashe akan abubuwa goma" 1. kun san Allah amma bakwa bashi haqqoqinsa, 2. kuna riya son manzonsa amma bakwa aikata sunnarsa, 3. kuna karanta Qur'ani amma bakwa aiki da shi, 4. kuna cikin ni'imar Allah amma bakwa godewa, 5. kuna cewa shaidan maqiyin Allah ne amma bakwa sa6a masa, 6. kuna cewa Aljannah gaskiya ce amma bakwa aiki da zai kai ku cikinta, 7. kuna cewa wuta gaskiya ce amma bakwa guje mata, 8. kuna cewa mutuwa gaskiya ce amma bakwa shirya mata, 9. kuna rufe matattun ku amma bakwa wa'azzantuwa, 10. kuna ta barcin ku kwananku yana qarewa amma kuna ta shagaltuwa akan aibanta wasu kuna manta aibinku. YA ALLAH KA AMSA ADDU'O'IN MU NA ALHERI BA DON AYYUKAN MU BA.
Comments
Post a Comment