mafusata

Mafusata Sun Yi Wa Sheik Yusuf Sambo Ya Sha Duka A Kaduna Daga Ibrahim Ammani, Kaduna Daruruwan wasu fusatattun matasa ne suka yi kukan kura, inda suka afkawa mataimakin shugaban majalisar malamai ta kasa, na kungiyar Izala, Sheik Yusuf Sambo Rigachikum, a yayin da ya halarci wajen rufe Tafsirin Al kur'ani mai girma wanda Dakta Ahmad Gumi, ke gabatarwa a masallacin Sulatan Bello da ke Kaduna. Kamar yadda Mallam Yusuf Sambo ya saba, yakan halarci karatun Tafsirin Kur'anin gabatarwa Dakta Gumi, a kowace rana da yammaci, saidai a ranar rufe tafsirin kwana guda bayan tashin tagwayen bama bamai da akayi a Kaduna, Malamin na shigowa, matasan wadanda kamar suna jiranshi suka afka mishi. Matasan sun rinka fadin cewa, Allah ya isa munafukin Malami, malamin Jonathan, a miko manashi mu aske gemunshi. Lamarin daya sanya dole jami'an tsaro suka shigo cikin masallacin domin magance al'amarin, kafin nan tuni wasu matasa har sun fara kai mishi duka gami da keta tufafin dake jikinshi. Da kyar jami'an tsaro sukayi nasarar fita dashi daga masallacin, bayan sun tarwats wadannan gungun matasa, wadanda ke ta faman Kabbara, suna fadin a basu malamin fada suyi maganinshi. Daga bisani an samu natsuwa a cikin masallacin, bayan da Dakta Ahmad Abubakar Gumi, yayi wa matasan magana, inda kowa ya koma ya zauna, sannan ya rokesu da suyi hakuri, kuma su martaba darajar malamin. Indai jama'a basu mance ba, a ranar Alhamis din makon daya gabata ne, shugaban kasa Goodluck Jonathan Jonathan, ya gayyaci wasu malaman addinin musulunci zuwa fadarshi, domin gudanar da bude baki, wanda Sheik Yusuf Sambo, da Sheik Dahiru Bauchi suka halarta, kwanaki shidda bayan wannan shan ruwa da sukayi ne, tagwayen Bama bamai suka tashi a Kaduna, wanda suka sanadin salwantar rayukan jama'a sama da dari

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA