mafarkina 1
Ina zaune tazo ta rufemin ido ta baya,can sai ta cire hannunta ta ruga da gudu cikin daki,na mike na bita da gudu ina zuwa muka fara wasa irin na masoya,tana jifana da matashin kai/pillow,nima ina jifanta dashi... Can sai na tashi naje wajenta,tana zaune bisa gado na duka domin na rungumeta, dukawata keda wuya sai naji na kwalla ihu nace,"wayyo Allah mama"...nan da nan mommy na da dad dina suka shigo dakina da gudu domin suga meya faru,suna zuwa suka ganni kwance a kasa na kone a kirji, basu ko tsaya jin meyafaru ba suka sungumeni zuwa asibiti.. Ina asibiti abokina mai suna Lawai yaxo gaisheni,to shine Lawai yake tambayana wai ya akai na kone? nacemai wlh na daura ruwa a risho domin in dafa indomie(abinka da mare mata)sai nadan kashingida kafin ruwan yai zafi, to kwanciyata keda wuya sai nafara mafarkin muna soyayya da ASABABU to a mafarkin nawane naje rungumeta sai akai rashin sa'a na rungume risho shine na kone a kirji. * to gwauraye da tuzurai idan za ai bacci a rinka nesa da risho ko hita kafin Allah ya kawo kudin aure
Comments
Post a Comment