lbr masoyiya. ta

Masoyiyata, abar qaunata, kuma sirrin rayuwata ta kasance sau da yawa takan qirqiro qarya domin ta kare kanta a duk lokacin da muka samu sabani a tsakaninmu, tsabar son da take yi min da gudun kada ta bata min rai ne yasa take yin hakan. Yau da gobe yasa a hankali na gano hakan, sai nayi tunanin me yakamata nayi ne? Shin in qyale ta ta cigaba tunda tana yine don ta faranta mini kokuwa? A qarshe na yankeshawarar in hana ta yin qarya, duk abinda ya faru ta fada min gaskiya kawai, indai zata yi qarya akan ta faranta min to kuwa lallai abinda yasa tayi laifin tun farko yafi qarfinta ne, sannan irin son da nake yimata da kuma yarda da ita da nayi na tabbata in tana da dama ba zata taba saba min ba. Tun daga lokacin dana kwabeta akan qarya sai yazamo duk ma abinda ya faru sai ta gaya min gaskiya; nikuma sai inji na fahimtu sai inyi mata afuwa. Bazan iya misalta muku irin QARFIN DA SOYAYYARMU ta qara ba saboda fadawa juna gaskiya, lallai bahaushe yayi gaskiya da yake cewa Gaskiya Dokin Qarfe Maqaryaci Ba Zai Hau Ba! Masoya ina kira gare ku da mu rike gaskiya a cikin soyayya kada son zuciya ko kuma wani karamin dalili ya sanya mu dinga yiwa junan mu qarya

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA