ladduba

WASU DAGA CIKIN LADUBAN DA SUKA SHAFI RANAR IDI 1. Yin wanka- Sa'id dan Jubair, yana cewa : "Abubuwa uku, sunnoni ne na idi : tafiya a kasa, da yin wanka, da cin abinci kafin a fita" 2. Cin abinci kafin a fita- An karbo daga Anas dan Malik ya ce : "Manzon Allah s.a.w. ba ya fita idin karamar sallah har sai ya ci dabinai kafin ya fita" 3. Yin kabbara ranar idi- wannan yana daga cikin manyan sunnonin ranar idi. Lokacin fara kabbara a idin karamar sallah shi ne : daren idi har zuwan liman ya shiga sallar idi. 4. Siffar kabbara- An karbo daga Ibnu Mas'ud -Allah ya yarda da shi – ya kasance yana kabbara a ranakun sha daya da sha biyu da sha uku na watan hajji, yana cewa : Allahu Akbar, la'ilaaha, illallah, wallahu akbar, Allahu Akbar, wa lillahil hamd" 5. Yiwa juna fatan alkairi (barka da sallah) An karbo daga Jubair dan Nufair ya ce : "Sahabban Annabi s.a.w. sun kasance idan sun hadu da juna ranar idi sashinsu yana cewa sashi : Allah ya karbi ibadunmu da ayyukanmu na alkairi. 6. Yin kwalliyar idi- An karbo daga Jabir -Allah ya yarda da shi – ya ce : "Annabi s.a.w. yana da wata riga da yake sanya ta ranar juma'a da ranar idi" Sahihu Ibnu Khuzaimah, don haka ya kamata mutum ya sa mafi kyawun tufafin da yake da su lokacin fita idi. 7. Tafiya ta wata hanyar da kuma dawowa ta wata hanyar daban – saboda Annabi s.w.a ya kasance yana saba hanyoyi ranar idi" Bukhari ne ya rawaito.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH