Jami'an Tsaro Sun Gano Wasu Makamai Da Aka Binne A Dajin Balmo
Jami'an Tsaro Sun Gano Wasu Makamai Da Aka Binne A Dajin Balmo Jami'an tsaro na kasa sun gano karin makamai da aka binne a cikin Dajin Balmo, wanda ya tashi daga Jihar Bauchi ya dangana da Jihar Jigawa. An kuma ce ya makwabci Dajin Sambisa wanda ke Jihar Borno inda 'yan kungiyar Boko Haram ke da sansanoni. Wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaron, Manjo Janar Chris Olukolade, ya fitar, ta ce sojoji suna tonon wadansu wurare ne a dajin da nufin gano makaman da aka binne lokacin da suka yi kicibis da manyan bindigogi goma, da bindigogi masu sarrafa kansu fiye da 80, da kuma jigidar harsasai da dama. Sanarwa ta kuma kara da cewa an kuma gano makaman harba rokoki da sauran kayan yaki masu yawa. Janar Olukolade ya kuma ce sojoji sun gano kayan jami'an tsaro ciki har da rigar kariya daga harbin bindiga
Comments
Post a Comment