izala

Kungiyar Izala Ta Yi Kira Ga Gwamnati Da A Kawo Karshen Cin Zarafin Da Ake Wa 'Yan Arewa Mazauna Kudancin Kasar Nan Kungiyar Izala ta kasa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen cin zarafin yan Arewa da ake yi a Kudancin kasar nan. Kiran ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar na kasa Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau a lokacin da yake gabatar da tafsirin safiyar Litinin (17 Ramadan) a garin Jimeta da ke Jihar Adamawa. Shugaban ya ci gaba da cewa Gwamnatin Tarayya ta gaggauta kawo Karshen cin Zarafin 'yan yankin Arewa da akeyi a kudanci yayin neman abinci cin su. Shehin Malamin yayi kiran ne jim kadan bayan da sojoji suka yi farauta tare da awon gaba da yan arewa a Safiyar Litinin a garin Yanagoa dake jihar Bayelsa Wadanda basu jiba basu gani ba, duk da zuwa yammaci an sako dukkanin wadanda aka kama ba tare da an samu wani da laifi ba. Babu nutsuwa ga mutanen Arewa a yayin zamansu a kudancin la'akari da abin da ya faru a jihohin Abia, Imo da na baya bayan nan a jihar Bayelsa bayan ance kasa daya al'umma daya. Daga karshe Shugaban yayi kira ga Maluma masu gabatar da Tafsirai a fadin Kasar nan da cewa su cigaba da tallafawa Marayu da gajiyayyu kamar yadda Annabi (SAW) ya kwadaitar mana. Mu tallafa wa Marayu sai muyi Tawassuli da shi domin Allah ya kawo mana karshen tashin hankalin da ke faruwa a kasar nan da sauran kasashen Musulmai da ke fadin duniya. "Inji Shugaban".

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA