hukunci
MENENE HUKUNCIN WANDA YACI ABINCI KO YASHA RUWA ABISA MANTUWA ALHALI YANA AZUMIN RAMADAN ??? AMSA ----- Sai yaci gaba da azuminsa yana nan bai karye ba, domin Allah ne yaciyar dashi ya shayar dashi. Daili kuwa ya tabbata daga Abi Hurairata (R.A) daga Manzon Allah (S.A.W) yace: "Idan mutum ya manta, yaci ko yasha, to sai yaci gaba da azuminsa, domin Allah ne ya ciyar dashi ya shayar dashi. ____________________________________ Kuduba Attarghib wattarhib na munzuri lahakikin sheikh Albany Juzu'I na farko shafi na (2). Suratul Baqarah, ayata183. Sahihul Bukhari hadisi mai lamba ta (1933). Dan Allah kuyi Like da share dinsa saboda yan uwanku su amfana. Allah ya hadamu acikin ladan baki daya.
Comments
Post a Comment