Azumi

FATAWOYIN AZUMIN RAMADAN. Tamtaba ta 64: MENE NE HUKUNCIN YIN AZUMIN SHIDA A CIKIN WATAN SHAWWAL (WANDA AKA FI SANI DA SITTU SHAWWAL)? Amsa: Yin azumin sittu-shawwal sunnah ce wadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wasallam) ya yi, kuma Sahabbansa suka yi. Haka kuma, magabata na kwarai sunyi. Hadisi ya tabbata daga Abu Ayyub al-Ansari (Radhiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wasallam) ya ce: "Wanda yayi azumin watan Ramadan, sannan kuma ya bishi da azumi shida a cikin watan Shawwal, to kamar ya yi azumin shekara daya ne 102." Sai dai ajwai wadanda suke ganin karhancin wannan azumin, kuma suna jingina wannan magana zuwa ga Imam Malik. Amma shi Imam Malik bai yi inkarin wannan Hadisin ba. Sai dai ya yi inkari ga wanda ba zai iya bambancewa tsakanin azumin Ramadan da Sittu-Shawwal ba. Watau don gudun kada ya hada su a jere da tunanin duk wajibi ne shi ya sa Imam Malik ya kara da cewa: Labari bai zo mini cewa magabatan Madinah suna yin wannan azumi ba. Domin tsoron wannan fitina ta kasa bambancewa 103. *NB*** 102. Sahih Muslim (1164). 103. Sharhi Sahih Muslim, na al-Kadi Iyad. 4/139-140, da al-Istidhkar, na Ibn Abdul Barr. 10/249. Wannan shine abinda Allah ya hore mana na Amsa tambayoyi, da fatan Allah ya Amfanar da mu kuma ya yafe mana kura kuran da mukayi a ciki. ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMAD, KAMA SALLAITA ALA IBRAHIM WA ALA ALI IBRAHIM. WA BARIK ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMAD, KAMA BARAKTA ALA IBRAHIM WA ALA ALI IBRAHIM INNAKA HAMIDUM MAJID. @ LITTAFIN SHAIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH (IMAM AHLUS SUNNAH WAL JAMA'AH).. Ya Allah ka sakawa malam da alkhairi da da sauran malamanmu, da muma gaba daya. Ya Allah Ka bamu ikon Amfana da abinda da muka ji ko muka karanta. Ya Allah ka sakawa iyayenmu da alkhairi, Ka shiryi zuriyarmu. Ya Allah ka taimaki Musulmi da Musulunci, ka kaskantar da Kafirai da Kafirci a duk inda suke. Ya Allah ka dawo mana da zaman lafiya a kasashen Musulmi, da garu-garuwansu, da gidanjenmu. Ya Allah Ka azurtamu duniya da lahira. Ya Allah ka samu a Aljannal Firdausi ka tsaremu daga wuta. Don Allah idan ka/kin samu lokaci ka/ki yi (sharing) din wadannan FATAWOYIN tun daga fitowa ta 1 har zuwa ta 25. Domin neman lada da falala a wurin Allah. Anan nake fatan yin sallama da ku muyi azumi lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA