another bornanza
haba jama'a, wai shin menene kesa bamu zurfafa tunaninmu, da kuma yin amfani da hankalinmu? har idan kamfanin Globacom zata kawo mana bonanza na idan kasa kudi zata baka garabasan fiye da kudin da kasa, har kaga muna tururuwan sa kudi kullum..... har idan kamfanin ETISALAT zasuke baku kyautan 15MB duk sati idan kunsa naira dari biyu......kai wani ma ko ana ha maza ha mata sai ya nemi kudi.....don more wannan garabasan!! to amma gashi an umurcemu dayin azumi shida a wannan wata na shawwal amatsayin BONANZA wanda yake rubanya lada da bamu garabasan samun falalan azumin wata biyu...wanda idan ka hada da azumin Ramadan da mukayi, muna sa ran samun falalan wanda ya shekara yana azumi.......amma mafiyawancinmu bamu bada hakan mahimmanci...... jama'a ina mana NASIHA har idan MTN da shauransu zasu ja hankulanmu, mai zai hana mufi karkata wajen samun rahaman ubangijinmu, muyi kokari mu ribaci wannan azumi na sitta shawwal.......
Comments
Post a Comment