allah subaha nahu wata ala yace

ALLAH (SWT) YACE: "HARAMUN NE KA SHIGAR WA IYAYEN KA, KO MUHARRAMANKA BA TARE DA YI MUSU SALLAMA BA" HATTA IYALANKA BA ZA KA SHIGA GARE SU BA SAI DA SALLAMA. (Q: NUR 59.) "Ya ku wadanda sukayi imani! Wadannan da hannuwanku na dama suka mallaka da wadanda basu isa mafarki ba daga cikin ku, su nemi izini sau uku, daga gabannin Sallar alfijir, da lokacin da kuke ajiye tufafin ku, saboda zafin rana, kuma daga bayan Sallar Isha'i. Su ne al'aurori uku a gare ku, babu laifi a kanku kuma babu a kansu a bayan su. Su masu kewaya ne a kanku, sashen ku akan sashe." (Surutun Nur, aya ta 58) A takaice ladubban shiga gida sune, dukkan yaron da ya balaga dane ko bawa, kada ya shiga gida ko dakin mahaifin sa ko uban gidan sa a a bayan sallama, har sai in an amsa da ya shigo, in ance ya koma, ya koma. In kuma yana zaton ko ba'a ji bane, to ya maimaita sau uku. Neman izini wajibi ne ga yayanka baligai a lokutan nan uku, kamar yadda yazo a aya ta 59, daga gabanin sallar Alfijir, lokacin tsakar rana, wato lokacin da ake ajiye tufafi saboda zafin rana da kuma bayan sallar isha'i. Wannan aya ta wajabta mana, musamman mata da su koyawa yayansu da kanne ko yan uwa dake zaune a gida tare da su da masu aiki, da su dauki tarbiyya irin wadda Al'qur'ani mai girma yazo da ita, da kuma sunnar manzon Allah tsira aminci su tabbata a gare shi. Halayyar mu ce a yanzu da aje wa mutum ziyara a ko wane lokaci, ko kuma a banka kai cikin daki babu sallama , in ba a amsa ba, sai mutum ya tafi yana fushi, yana kunkuni wai anyi masa wulakanci. Ya 'yan uwa Musulmi, mu ji tsoron fushin Ubangiji bana mutum ba, fushin Mutum ko zagin sa, bazai cutar da kai da komi ba. Yayin da ka bi dokar Ubangiji, to zakayi rayuwar ka cikin kwanciya hankali babu kunci. Sannan ina Nasiha ga yan uwa maza da su daina zuwa gidajen abokai a lokutan Da Allah ya hana. "Babu laifi a gare ku da kuci abincin juna, ko 'dai 'dai, ko a kwano daya, a gidajen kawunan ku, 'yan uwanku har da abokan ku, amma in anci a tashi, kada a tsaya hira, kuma kada aje kafin lokacin da aka gayyace ka, ka zauna har sai an gama abincin, wannan baya halatta, yayin da muka bi dokar Allah, to baza mu sami kuntata a kanmu ba, insha Allah. Yana daga dabi'un mu a yanzu a ki watsewa bayan gayyata, ko bayan aboki yaci abinci, sai ya tsaya hira, har masu gida su kosa. Bahaushe yace, wai bayan ci zama tsegumi, tafiya rashin kunya, to umurnin Allah zaka bi ko son rai? Shima bahaushen ai cewa yayi zama tsegumi, wanda yake haramun ne, cewa kuma tafiya rashin kunya, shima kuskure ne, domin yaci karo da umurnin Allah. Allah ya samu a bisa hanya madaidaiciya, ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon binta, ya nuna mana karya karya ce ya bamu ikon guje mata.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA