alheri danko
ALHERI DANKO NE BAYA FADUWA KASA BANZA.. Wani mutum ne ya hau mota irin hayis dinnan zashi wani waje sai da yazo sauka saiya duba domin ya biya kudin motar sai kuwa yaga babu kudin da yake aljihun sa. ya duba ya duba amma yaga babu kudinnan,nan da nan kwandastan motar ya fara surutu yana zage zage wai dama irin halin wasu mutanen kenan sai su hau mota basu da kudi suce wai kudin sun fadi. mutuminnan yayi rantsuwa da Allah akan kudinnan faduwa sukayi, amma kwandasta da direba suka ki yarda suka ce ai sai ya biya ko kuma suyi masa dukan tsiya. mutuminnan har ya fara hawaye saboda takaicin sunce masa barawo ne shi kwandastan ya sauko daga motar ya shake masa wuyan riga zai fara yi masa duka. sai wata mata acikin motar tace su dakata,ta dauko kudin motar mutumin ta biya masa sannan ne kwandastan ya kyale shi. mutumin ya dubi matar nan zai mata godiya,sai tace masa''karka damu kaima ka kyautata wa wanda kaga yana neman taimako''a haka suka ja motar suka tafi bayan kwana biyu mutuminnan yana cikin tafiya sai yaga wani mutum agefen hanya an masa jina jina da alama kwace akayi masa. sai mutumin ya dauke sa ya kaisa gidansa nan da nan yaje ya samo ruwa ya yayyafa masa sannan ya bashi ruwan yasha bayan ya dan dawo hayyacin sa, sai mutumin ya kawo masa abinci yaci, sannan ya dauko masa wasu kayan ya canza na jikinsa ya bashi takalmi ya saka. da mutumin ya samu nutsuwa sai dubi wanda ya taimaka masa sannan yace''amma ban san da mai zan saka maka ba domin ka taimake ni,da baka taimakeni ba ka dauko ni da mutuwa zanyi a wajen da ka ganni''da mutumin nan yaji haka sai ya tuna da maganar matar nan data taimake shi alokacin da kudin sa suka fadi sai ya dubi wanda ya taimakwa dinnan. yace''karka damu kaima ka taimakwa wanda kaga yana neman taimako'' ashe wanda aka taimaka dinnan shikuma likita ne a wani asibiti. rannan yaje asibiti sai yaga ankawo wata yarinya karama bata da lafiya kuma rashin lafiya mai tsanani domin in ba,a yi mata aiki ba da gaggawa to tabbas saidai tamutu. kuma gashi an gaya wa babar yarinyar kudin aikin tace bata da su. sai ya tuna da alherin da mutumin nan yayi masa saboda haka sai shima ya biya wa yarinyar nan kudin aikin nan aka yi mata aikin babar yarinyar tazo har ofis dinsa domin tayi masa godiya amma sai ya dube ta. yace''karki damu kema ki taimakawa wanda kika ga yana neman taimako'' ashe matar nan itace wadda ta fara taimakawa mutuminnan ta biya masa kudin mota a sanda kudin sa suka fadi, shine yarta bata da lafiya kuma bata da kudin da za.a yiwa yar aiki. wannan likita ya biya kudin nan. ikon Allah kenan kunga alherin da tayi yayi yawo karshe kuma ya dawo kanta yan uwa mu dinga yin alheri domin alheri danko ne baya faduwa kasa banza.
Comments
Post a Comment