aku da matar uban gidansa
AKU DA MATAR UBAN GIDANSA
Wata rana wani attajiri za shi fatauci sai ya bar matarsa agida yana da wani aku. Sunnan tare sai matar ta rika fita yawao don taga mijin bayanan. Barorin gida da suka ga abin damesu basu da dammar yin Magana kada matar nan ta sare su wajen mai gida in ya komo. Saboda haka suka zura ido
Ana nan ran nan sai maigida ya dawo . kasan a;la amrin doniya bashi boyuwa , sai wani tsegunta masa abin da matarsa tayi ta aikatawa bayan bashi nan yaji haka, sai ya kiar matar ,yasameta yayi ta zagi. Ya dauki sanda kuma yabata kasha.
Da matanan nan taga haka sai tayi yaji , aka koma da ita. Tace a ranta , “ Ba wanda ya fadi sai aku “ kasan mu , Allah yabaka nasara , bakin jini garemu kwarai , tum ba game da mataba. Suna cewa mu fiya tsegumi . Saboda haka , ta bari mai gida ya tafi kasuwa , sai takama aku, tafige shi da rai ,ta wurga shi waje ta taga , tace, “ daga gareni kabar
Tsegumi “ Allah yasa aku bai mutuba , ya tsallaka har yakai hurumi ya sami kabarin ya shige , yayita jiyya .
Da mai giodan nan ko ya dawo , sai matar wai bayan fitarsa kadan kyanwa ta cinye aku. Ko da yaji haka sai ya san karya takeyi , kasha shi tayi , don tana tsammanin shi ya gaya masa tana fita da ba shin an . saboda haka fusata kwarai da gaske , ya kama ta duka kamar bazai barta ta da raiba. Ya kore ta daga gidan, ta tafi wajan hurumin nan tana kuka . Ashe aku na nan kusa da ita cikin wani kabari . yana ji.
Sai yace mata.’’Yi shiru , bari kuka , in Allah ya so kya koma dakinki . Amma akwai sharadi guda, kije ki aske kanaki sarai , sa’an nan ki dawo nan ,gobe zan taimakeki ki koma .”
Matan nan ta duba , bata ga kowa . Abika da mace , sai tayi tsammanin wani matacce ne ke yi mata mgana . Nan da nan ta tafi gidan iyayenta , aka aske mata kai. Da gari yawaye , maraice yayi ta nuwo wajen hurimi, kai na kalli sai kace na namiji.Da isowarta sai ta tafi wajen kabarin. Abinka da jahila ta durkusa , tace ,”Na asko.
Sai aku tace , “ to, kin san dalilin dayace ki aske kanki domin kin zalunci wani dan tsuntsu , kika zarge shi akan abin da bai jib a bai ganaba , har kika fige da ransa , kika wurgo shi bayan gida. A wannan nayi miki sauki , nace ki aske gashin kanki kawai , amma in kin kuskura kika kika sake yiwa wani tsunstu haka, ki kuka da kanki. Amma akun nan da kika kasha zai koko duniya, yadda zan mai dake dakinki ,shi kuma zan mai dashi gareki. To, ki lura das hi kyau , kisa mijinki ya ajiye yaro guda mai hankali wanda zai rika lura da shi, a rika bashi ruwa da sukari. Kuma ki tsawatawa yara su bar kiran sa aku kuturu .”
Mtan nan takara dukawa , tace, “Naji.”
Da zata tashi sai aku yace, “Dasaura. Yau kinga sha biyu ga watan safar . To, ko wacce shekara sha biyu ga watan safar ki aske kanki , don ya rika tuna miki aku da da ki ke ganinsa banza-banza ba banza bane.
Amanar Allah ce yasa a hannuku ‘yan adam , yafi kyau kuwa ku lura ita da kyau.watan duk da yazo baki aske kanki ba. Yadda na gaya miki yanzu,tabbatabaki shekara. Shi ken an, gobe kya koma in sha Allahu. Tafi gida abinki. Amma ki kiyaye gargadin nan da yimiki, ki kuwa kirki ,kibi mijinki sau da hannu. Allah yagama muda alheri a
Darassalamu!”
Mace Takoma Gidan Su aku Yatashi yana Tsale har yakai Gidan Tajirin Nan Yace Masa “KA SA NI”
Ta jirin ya dubi aku ba gashi yace yaya zanyi insanka bantaba ganin ka ba.
Aku y ace “baka taba Ganina ba ? ai nine akunka wada kyanwa tacinye.
Tajiri yace “tunda kyanwa taciyeka yaya kuma kafara har kayi rai? Dama dai ba Kyanwa Tacika ba akwai yadda akayi.
Aku Yace “daga cikin Kyanwar aka Nufa infitu don Inshaida maka Duka abin da matarka ta fadi na batun kyanwa ta cinye ni gaskiya ne. kada ka zargeta amma In kana sona zankara dakatawa kuma wurika in yi gashi in koma kamar da, har allah ya kari kwanana gabadaya .amma sai ka Maiyar da matarka ka yafemata kuyi zaman lafiya .
Mai gida yace,To ya aika matar ta dawo,ya gafarta mata suka sake zaman su .daga ra nan tazama matar kirki duk garin ba wada akeso sai ita don kirkinta
Ina fata mai karatu ya dauki darisi akan wannan labari
Comments
Post a Comment