ABUBUWAN DA SUKE RUSHE MA MUTUM LADAN AZUMINSA:
ABUBUWAN DA SUKE RUSHE MA MUTUM LADAN AZUMINSA:
Malamai sunce akwai wasu ayyukan Zunubi wadanda duk da cewa basu karya Azumi, amma suna rushe ladansa.
Wadannan abubuwan sun hada da:
1. QARYA: Qirkirar labarai na Qarya domin ayi dariya, ko kuma domin wata manufa wacce bata inganta ba.
2. QAULUZ ZOUR da kuma aiki dashi : Maganganu marassa tushe yayin da aka dangantasu da wani wanda bai ji ba, bai gani ba.
3. QAZAFI: shima wani nau'I ne na Qarya da ake yi domin 'bata sunan Mutane. 4. GULMA : Shi ma wani nau'I ne na Qarya da Qauluz Zour.
5. ANNAMIMANCI: daukar magana daga wajen wani, ka kaita wajen wani da niyyar 'bata tsakaninsu, ko kuma don neman shiga awajen wani.
6. RANTSUWAR QARYA : ita ma nau'I ne na Qarya da Qauluz Zour. Yazo acikin hadisin Bukhary: "Duk wanda bai bar Qauluz Zour da kuma aiki dashi ba, to babu ruwan Allah don yabar cin Abincinsa da shan abin shansa
Comments
Post a Comment