A wata ruga
A wani rugar fulani ne an hadu za'ayi meeting da daddare, sai aka rarrabawa mata kyadir da ashana kowacce ta kunna a kan teburin da mijinta zay zauna. Aka ba wa matar Sarkin Ruga ma nata domin ta kunna a teburin mijinta kafin ya iso. Daga zuwan sa sai ya ga hasken kyandir akan kowanne tebur amma banda nasa. Nan da nan ya fara masifa, Sarkin Ruga: in banda iskanshi yaya za a she teburin kowa da haske amma banda nawa? Masu rabo: A'a ranka ya dade mun ba matarka kyandir da ashana ta kunna a teburinka. Sarkin Ruga: ke ina kyandir din da ashana da aka baki? Mata: A'a an bani ashana amma ban ga a-shi-balbal din ba. Masu rabo: Ba a-ci-balbal ba, wannan farin abun mai zare da muka baki. Mata: Oho...aradu ina she ROGO ne, she na shinye!
Comments
Post a Comment