tambaya mabudin ilimi

assalamu alaikum Allah ya kara wa malam lafiya ameen tambayata anan itace ya hallata idan miji yana wasa da matarsa ya umurceta data tsotsan mai xakarinsa ko kuma idan suna kwance da matar sai mijin yakama tsotar wa matar farjinta. nagode malam (Daga wata Baiwar Allah). AMSA **** A'a gaskiya ba za'a iya cewa Haramun bane kai tsaye saboda rashin Nassi wanda ya haramta hakan. Sai dai Mafiya yawan Malamai sun Karhanta yin hakan kuma Sunce yin haka ya kauce ma FITRAH (wato ainihin tsarin da Allah ya halicci bayinsa akai). Shaykh Nasiruddeen Albany ya buga wani misali: Yace koda acikin dabbobi babu wadanda zaka ga suna yin irin wannan alokacin Jima'I in banda aladu (Alhanzir). Kuma shi abisa fahimtarsa haramun ne Namiji ya sanya al'aurarsa acikin bakin Matarsa. Hakanan itama matar, haramun ne Namiji ya rika tsotsar Farjinta. Shi dai baki an halicceshi ne ajikin Dan Adam domin yin zikiri da karatun Alqur'ani da sallah da kuma addu'a da cin abinci.... Amma ba'a halicceshi domin yin Jima'I ta nan wajen ba. Tsotson al'aura yakan sanya wani abu ya fito daga al'aurar kamar misali Maniyyi ko Maziyyi. Idan Maniyyi ne, to Makruhi ne shansa. Amma idan Maziyyi ne, to HARAMUN NE. Allah yace : "KUZO MUSU (Ku sadu da matayenku) TA WAJEN DA ALLAH YA UMURCEKU". To ta ina ne Allah yace ayi Jima'I?? Kowa yasan dai ta farji ne ba ta baki ko dubura ko wani waje daban ba. Da fatan za'a kiyaye. Wallahu a'alam.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA