shehu jaha

`°•.¸¸.•°` `°•.¸¸.•°` `°•.¸¸.•°``°``°•.¸¸.•°

Daga hikayoyin SHEHU JAHA

Shehu jaha ya saba kullum ya sayo , ganyaye (na ci) da kuma kayan marmari ya kawo gida, ita kuma matarsa ta saba ta dafa ganyayen da kayan marmarin kuma ta
aika wa kawarta kyauta!
Kullum dare idan Jaha ya hakimci don ya kwashi girki da kayan marmari, ba abin da matar nan take kawo masa sai gurasa tsura! Abin dai yana ta daurewa Jaha kai.

Rannan dai sai ya yi ta maza; ya tsaga
bullensa ya tambayi matar:

“Wai ni ina ganyaye da kayan marmarin da nake shigowa da su kullum; ina kike kai su?” Sai matar ta kada baki ta ce:

“Abin da ka samu ka godewa Allah wannan shi ne rabonka!!! duk lokacin da na dafa wani abu MAGE take cinyewa”. Shehu jaha ya dan tsaya tsai yana tunani akan
maganarta, sannan sai ya yi wuf ya zabura ya dauke GATARINSA da yake rataye a jikin garu ya wurga shi cikin
akwati ya garkame. Sai matar ta tambaye shi: “shehu lafiya menene na buye gatari kuma?”

Sai ya ce: “Na boye shi ne don kada mage ta gani ta cinye!

“Sai matar ta cika da mamaki, har ta yi wata irin shewa ta ce:

“Mahaukaci ne kai! Mage tana cin gatari ne!! “Sai shehu jaha ya ce mata:“Wallahi da hankalina
sarai, amma ke me kike gani; yanzu magen da za ta rika cinye girkin dirhami goma, da kayan marmari na dirhami goman (ashirin kenan),

INA GA GATARIN
DIRHAMI UKU!!

Comments

  1. kunjungan perdana dimalam hari sobat, semoga menjadi awal yg lebih baik :grin:

    ReplyDelete
  2. innine xanyi binkice akai

    ReplyDelete
  3. Innine sai nayi sati bana kawomata idan ta tambaya sai nace rabontane babu

    ReplyDelete
  4. INNINE ZANSAKE SAWOWA DAN INKAMATA DAHANNU TAJIKUNYA

    ReplyDelete
  5. Masha Allahu

    ReplyDelete
  6. Allah yakara basira26 July 2016 at 12:09

    Allah yakara basira

    ReplyDelete
  7. zankara sawowa don inkamata

    ReplyDelete
  8. yakamata ku bawa jaha shawara yayi sati uku baya dawowa inya dawo tace meya faru saiyace "ina tsoro kar in dawo mage ta cinye ni"hah hah hah

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA